Home Siyasa Da umarnin Kotu muka kwashe motoci daga gidan Matawalle – Gwamnatin Zamfara

Da umarnin Kotu muka kwashe motoci daga gidan Matawalle – Gwamnatin Zamfara

309
0

Gwamnatin Zamfara da ke arewacin Najeriya ta ce da umarnin Kotu aka kai samame tare da kwashe motoci 40 a gidan tsohon gwamnan jihar Muhammed Bello Matawalle.

Gwamnatin na wannan kalamai ne a matsayin martani ga tsohon gwamnan da ya zargi gwamna Lawal Dauda Dere da jagorantar afka wa gidansa aka kwashi motoci.

A wata hira da ya yi da BBC tsohon gwamna, Bello Matawalle ya yi zargin cewa baya ga kwashe motocinsa na hawa, an kuma wawushe ɗakunan matansa tare da zargin cewa Gwamna Dauda ne ya jagoranci samamen.

Sai dai, babban mai ba gwamnan Zamfara shawara kan harkokin watsa labarai Mustapha Jafaru Kaura, ya shaidawa BBC cewa ce jami’an tsaro ne suka kai samamen a gidan tsohon gwamnan bayan samun umarnin kotu.

“Umarni aka bayar ko can baya, an je wurin kotu kuma ta ba da umurni aje gidansa na nan Gusau, da kuma wanda ke Maradun domin a ɗauko motocin”.

‘Babu gaskiya a kalaman Matawalle’

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce duk motocin da aka dauko daga gidan tsohon gwamnan, na gwamnatin ne.

Ta kuma karyata zargin da Matawallen ya yi akan cewa an dauki motoci masu dauke da hoton shi da shugaba Tinubu.

Sai dai tun farko tsohon gwamnan jihar Zamfara ya musanta ikirarin da mahukutan jihar suka yi a kan cewa adadin motocin da suka dauko ya kai 40. Sannan ya ce akasarin motocin da aka kwashe daga Amurka ya siyo su.

A yanzu mahukunta jihar sun ce ‘yan sanda ne suka kirga motocin bayan da aka ɗaukosu.

Sun kuma karyata ikirarin da Matawalle ya yi a kan cewa jami’an tsaro ne su ka kai samamen gidansa karkashin jagoranci kwamishinan ‘yan sanda da kuma sabon gwamnan jihar, Lawal Dare.

“Me Dauda Lawal zai je ya yi a gidan shi? Me ya haɗa Dauda Lawal da zancen daukar mota?” kalaman Mustapha Jafaru.

‘Za mu ci gaba da ƙwato kadarorin gwamnati’

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta fitar da wata sanarwa ita ma, tana mai cewa za ta ci gaba da bincike da kwato motocin gwamnatin da aka zargin tsohon gwamnan da sace wa.

Sanarwar da ‘yan sandan suka aike wa BBC ta ce duk wanda yake ganin an karbe motar da ba ta gwamnati ba ce, to ya kawo takardar shaidar cewa motarsa ce a mayar masa.

Wannan dambarwa tsakanin tsohon gwamna da ɓangaren sabuwar gwamnati ta ja hankali ‘yan Najeriya, musamman zarge-zarge da Matawalle ya yi bayan afkawa gidansa.

Tun kafin wannan lokaci gwamnan Lawal Dere ya ke ta sanar da cewa Matawalle ya wawushe dukiyoyin gwamnati da motoci inda aka bukaci ya gaggauta mayar da su.

Sai dai Matawalle ya yi biris yana mai cewa ana yi masa bita-da-kullin siyasa, lamarin da ya tilasta kai wannan samame bayan gargaɗin da aka rinka fitarwa a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here