Home Labaru masu ratsa Zuciya ‘Da na shigo gida sai ɗana ya fashe da kukan yunwa’

‘Da na shigo gida sai ɗana ya fashe da kukan yunwa’

160
0
foodstuff

Magidanta masu ƙaramin albashi a Najeriya, na ci gaba da kokawa a kan matsi da ƙuncin rayuwar da ɗumbin mutane a ƙasar suka shiga.

Hauhawar farashi da tsadar rayuwa da kuma ƙarancin kuɗi, sakamakon janye tallafin man fetur da tsadar dalar Amurka, sun haɗu sun jefa al’umma masu yawa a ƙasar cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

Farashin kayayyaki ya ninka fiye da sau uku, yayin da sufuri ya zama wani babban lamari da mutane ke kashe maƙudan kuɗaɗe a kai.

Malam Kabiru Garba, wani ma’aikaci ne mai ‘ya’ya shida, da ya dogara a kan albashin naira dubu 55 a ƙarshen wata, ya shaida wa BBC cewa a baya kuɗin na isa ya yi duk wata hidimar gida, amma a yanzu, wasu lokuta, sai a kwana ba a ɗora tukunya a gidansa ba.

”Da ina sayen buhun shinkafa da katan din taliya, kuma za su yi min wata cif kafin albashi (watan gaba) ya zo amma yanzu ban isa ba, domin idan na sayi shinkafa buhu ɗaya, albashina bai fi saura dubu 10 ba”.

A cikin makon jiya ne, Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ta sanar da shirin gwamnatin na bai wa jihohi naira biliyan biyar da tirelolin shinkafa 180 domin rage wa masu ƙaramin ƙarfi raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Majalisar ta ce jihohin za su yi amfani da naira biliyan biyar ɗin ne domin sayen buhunan shinkafa 100,000 da masara da kuma takin zamani, waɗanda za a raba ga talakawa.

Sai dai har yanzu talakawan ƙasar kamar Mallam Kabiru Garba na kukan cewa ‘ya’yansu na kwana da yunwa saboda rashin abin da za su ba su.

Magidancin ya kara da cewa a halin yanzu da wuya yake yin cefane da sayen itace da man girki, balle ma a yi maganar kuɗin makarantar yara.

”A kullum, sai mun ci garin kwaki, ko rana sau ɗaya ko sau biyu shi ne mafi sauƙi, abin da aka samu za a ci, idan ba a samu ba sai a yi haƙuri a kwana da yunwa,” in ji shi.

Su ma wasu magidanta sun faɗa wa BBC a Kano cewa ko da an biya su albashi, da ƙyar suke cefanen kwana 15 a gidajensu.

Malam Auwalu Rimin Kira ya ce ya yi ritaya daga aiki tsawon sama da shekara ɗaya kuma yana da ‘ya’ya 12. amma har yanzu bai samu haƙƙoƙinsa ba.

”Ina ɗaukar albashi na lafiya lau, amma yanzu ga shi na yi ritaya, sai mu yi kwana da kwanaki yanzu ba mu ɗora abinci ba a gidana.

Sai na shiga gida ka ga yaro ya fashe min da kuka,” in ji shi.

Majalisar Tattalin Arziƙi a Najeriya dai ta kuma ce la’akari da halin da ake ciki da kuma ƙudurin gwamnati na shawo kan tashin gwauron zabi da farashin abinci ke yi, ya sa gwamnatin tarayyar a baya-bayan nan ta ba da tirelolin shinkafa biyar-biyar ga kowacce jiha.

Tuni dai ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya suka fito suka soki matakin bai wa gwamnoni maƙudan kuɗaɗen, don raba wa jama’a a matsayin rage raɗaɗin cire tallafin mai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here