Home Siyasa Da Ga Karshe Tinubu Ya Kai Sunayen Ministoci 28 Zuwa Majalisar Datttawa

Da Ga Karshe Tinubu Ya Kai Sunayen Ministoci 28 Zuwa Majalisar Datttawa

219
0

yayin da yan Najeriya suka shafe watanni biyu su na jiran jerin sunayen ministoci yau Alhamis Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya karanta sunayen mutum 28 da ga cikin 36  da doka ta amincewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya aike musu.

Sunayen wadanda a ka gabatar ga Majalisar sune kamar haka:
1. Abubakar Momoh
2. Amb. Yusuf Tukur
3. Ach. Ahmed Dangida
4. Bather Hannatu
5. Uche Nnaji
6. Dr.Becha Edu
7. Dr. Doris Ngoko
8. H.E David Umahi
9. H.E. Ezenwa Wike
10. H.E Nasiru El-rufa’i
11. H.E Abubakar Badaru
12.Rtd. Hon. Ekoh
13. Hon. Nkiru Nwochocha
14. Olubumi Tunji Ojo
15. Stella Okjeta
16. Hon. Ojo Kenedy
17. Bello Muhammad Gordon you
18. Dele Alake
19. Lateef Fagbemi
20. Muhammad Idris
21. Oluwale Edu
22. Waheed Adebayo Adalabu
23. Mrs. Iman Sulaiman
24. Ali Pate
25. Prof. Joseph
26. Sen. Abubakar Kyari
27.John Eno
28. Sani Abubakar Danladi
Wadannan jerin sunayen da Shugaban kasar ya gabatar, Majalisar Datttawa zata tantance su sannan ta sake mayar masa da sunayen domin ya amince da da su.
Ko da ya ke ba a cika samun Majalisar tana kin tantance sunan wani da ga cikin sunayen da Shugaban Kasa ya aike da su ba  in banda lokacin Obasanjo da Majalisar taki amincewa da Borishade da ga Osun da Sereki da Jihar Lagos.
Akwai kyakkyawan yakini cewa duka sunayen da Shugaban kasar ya gabatar Majalisar za ta amince da su ba tare da wata matsala ba.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai sanar da guraben da ya tura kowanne minista a kalla a cikin sati daya domin su kama aiki a ma’aikatun na su ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya  ce sauran sunayen ministocin za a kawo da ga baya.
Sai dai Majalisar tace zata rufe kofa don ta yanke shawara ko zata amince da sunayen cikin sati mai zuwa ko sai ta dawo da ga hutu da za ta tafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here