Home Lafiya Cutar Mashako: Majalisar Dattawa Ta Umarci Hukumar NCDC Da Su Gaggauta Dakile...

Cutar Mashako: Majalisar Dattawa Ta Umarci Hukumar NCDC Da Su Gaggauta Dakile Yaduwa Cutar

253
0
Sen. Khaleel, Kd

Majalisar Dattawa ta Umarci Hukumar kula da Yaduwar Cututtuka ta Kasa, NCDC da su gaggauta fito da matakai da za su dakile cigaba da yaduwar cutar Mashako wacce aka fi sani da Dyptheria a jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne ranar Laraba lokacin da Dan Majalisar Dattawa da ga Jihar Kaduna, Sanata Ibrahim Khalid ya gabatar da kuduri na gaggawa akan Cutar.

Ya ce daukar matakin gaggawa ya zama dole ganin yadda cutar ta ke ta yaduwa kuma tuni ta kashe sama da mutum 20 a Jihar Kaduna. In da ya ce , ya kamata a dauki mataki na ganin cutar bata cigaba da yaduwa zuwa wasu Jihohi da suke da makwabtaka da Jihar ta Kaduna ba.

Sanata Khalid ya ce Majalisar Dattawa ta nuna damuwarta akan batum kuma Yan uwansa Yan Majalisa sun nuna damuwar su, inda suka bayar da gudunmawa wajen ganin Majalisar ta shiga cikin lamarin.

Ya ce nan take Majalisar ta amince da Kudurin tare da bayar da umarni da Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa wato NCDC ta su gaggauta bincike akan cutar tun da har yanzu ba bu cikakkiyar masaniya akan cutar tare da daukar matakai da za su dakile yaduwar cutar a kasarnan.

Sanata Khalid ya yi kira ga Hukumar Wayar da Kai ta Kasa wato NOA da ta gaggauta fito da shirye shirye na musamman don ilimantar da Jama’a akan cutar.

In da ya ce akwai karancin sani akan cutar sabo da haka hakkin Hukumar ne na su wayar da kan jama’a akan ta don gudun yaduwar ta.

Sanatan ya ja hankalin al’umma da su dauki matakin kariya ta hanyar tsaftace hannayen su da rufe bakin su da takunkumi tun da cutar an ce ta na yaduwa ne ta iska. Sannan ya ce su saurari shawarwarin masana akan cutar don daukar matakai da za su hana yaduwa ta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here