Home Muhalli Majalisar Dattawa Ta Roki Gwamnatin Taraiya Da Ta Gaggauta Gina Dam A...

Majalisar Dattawa Ta Roki Gwamnatin Taraiya Da Ta Gaggauta Gina Dam A Najeriya

145
0
20231106 152308

Majalisar Dattawa ta roki Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta gina Dam a Najeriya domin dakatar da rasa rayukan daruruwan mutane da biliyoyin nairori a kasarnan. 

Majalisar ta yi wannan roko ne ranar Litinin a wani zama na gaggawa da ta kira mambobinta inda dan Majalisar Datttawa mai Wakiltar Adamawa ta tsakiya,Sanata Aminu Iya ya gabatar da kudurin neman a dakatar da rasa rayuka da a ke yi a kasarnan haka.

Sanata Iya ya ce sakamakon sako ruwan Dam  da ga kasar Kamaru ta ke yi a duk shekara sai Najeriya ta rasa rayuka na daruruwan Yan kasar a dalilin ambaliyar ruwa.

Ya ce bara an rasa rayuka na sama da mutum 200, in da a satin da ya gabata ma, a yankin sa mutum 30 sun nutse a kogin wanda hakan ya jawo rasuwar mutum 7, an ceto mutum 5, sauran kuma a na neman su a lokacin da mu kehadawannan rahoton.

Sabo da haka ne Sanata Iya ya nemi gwamnatin Taraiya da ta gina Dam cikin gaggawa don a dakatar da asarar rayuka da dukiya da a keyi shekara da shekaru a Najeriya.

Sanata Iya ya kara da cewa akwai yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya da kasar Kamaru cewa bayan da Kamaru ta gina nata Dam din shekarun da su ka gabata Najeriya ma za ta gina ita ma na ta Dam din amma har ya zuwa yanzu Najeriya ba ta gina na ta Dam din ba.

Majalisar Dattawan ta amincewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya saka kudin gina Dam din a cikin kasafin kudi na shekara ta 2024 domin a fara gina Dam din cikin gaggawa.

Har ila yau Majalisar ta bukaci Shugaban kasar da ya kai dauki na gaggawa ga al’umar Jihar Adamawa wadanda suka rasa rayuka da dukiyoyi masu tarun yawa a sakamakon ambaliyar ruwan Dam din.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here