Home Diplomasiyya Cire Takunkumi: Kasashen Nijar, Bakina Faso Da Mali Ku Zo A Zauna...

Cire Takunkumi: Kasashen Nijar, Bakina Faso Da Mali Ku Zo A Zauna A Tebirin Sulhu – Inji Sanata Wadada

116
0
IMG 20240228 181216

An yi kira ga Kasashen nan guda uku da su kayi juyin Mulkin Soja wato  Nijar da Bakina Faso da Mali da su rugumi cire takunkumi da Kungiyar Tattalin Arzikin Africa Maso Yamma ta yi mu su su zo a zauna a teburin shawara don warware matsalolin da ke tsakanin su.

Wannan kira  ya fito ne da ga bakin Sanata Aliyu Wadada dan Majalisar Datttawa da ke Wakiltar Jihar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Taraiya hirarsa da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Abuja a ranar Laraba.
Ya ce ya kamata kasashen su mutumta karamcin da Kungiyar ECOWAS ta yi musu na cire takunkumin sakamakon kiraye-kiraye da a ke yi wanda Kungiyar ta amsa duk da cewa juyin mulkin Soja da kasashen su ka yi ba a bu bane da duniya ke so a wannan zamani.
Wadada ya ce ba daidai bane Shugabannin juyin mulkin da su rinka zagin Shugaban kasar Najeriya domin hukuncin da ya dauka ya yi shine a matsayin sa na Shugaban Kungiyar Kasashen Tattalin Arzikin Africa maso Yamma a lokacin da ya dace.
Sanatan ya ce yanzu da aka cire takunkumin ya kamata su mutumta hukuncin Kungiyar su zo a zauna don a lalubo mafita sabo da alfanu da kasashen su ke samu a matsayin su na tsintsiya madaurinki guda.
Ya ce Najeriya da Nijar yan uwan juna ne kuma suna amfana da kasancewar su tare ta fannoni da dama kamar tattalin arziki da taimakekeniya ta fannin tsaro da ma aurataiya da sauran su.
Sabo da haka ne ya ga ya dace da ya yi wannan kira a matsayin sa na Dan siyasa mai cin  moriyar siyasa kuma ita ma siyasar ta na cin moriyar sa. In da ya kara da cewa  mulkin soja abu ne da ake kyamatar sa a duk duniya.
Sanata Wadada ya yi kira ga Kasashen da su gaggauta shirya zaben sabuwar gwamnati ta siyasa domin ita ake da bukata a wannan lokaci ba mulkin soja ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here