Home Siyasa Cire Takunkumi Kan Wasu Kayayyaki: Wata Kungiya Ta Yabawa Shugaba Tinubu

Cire Takunkumi Kan Wasu Kayayyaki: Wata Kungiya Ta Yabawa Shugaba Tinubu

157
0
President Tinubu 6

Kungiyar Kishin Cigaban Matasa da Zaman Lafia wato “Concern Mind for Youth Empowerment and Peace Development Initiative” ta ya bawa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu a sakamakon cire takumkumi day a yiwa wasu kayayyaki 43 a wani mataki na saukakawa Yan Najeriya.

Shugaban Kungiyar Alh Habibu Sani Kano ne ya yi wannan ya bo a wata sanarwa da Sakataren Kungiya Comr. Aminu Shehu Azare ya sakawa hannu in da ya ce cire takumkumin zai saukakawa Yan Najeriya matsi na tattalin arziki tare da daidaita farashin kayan abinci wanda ya yi tashin gwauron zabi.

Alh Habibu Sani Kano ya roki Gwamnatin da tayi duk mai yiwa wajen ganin Babban bakin kasa wato CBN ya cika dukkan ka’idodin baiwa yan kasuwa dukkan gudummawar da suke bukata batare da an samu tseko ba.

Ya ce, wannan shine zai taimakawa Yan kasuwar bayan haka ya kuma sa kayan abinci ya wadata a kasarnan.

Har ila yau, ya jawo hankalin yan kasuwar da suji tsoron Allah su kaucewa shigo da gurbatattun kaya kana su yi dukkan maiyuwa wajen kare martabar kasarmu Najeriya .

Habibu Kano ya roki gwamnatin da ta tabbatar da tsarin nan na sanya idanu akan dukkan wasu ayyuka da gwamnatin ta bijuro da su na raya kasa, wannan ne zai baiwa gwamnatin damar sanin al’amuran da ke gudana mutuka gaya.

Bayan haka ya roki gwamnatin da ta dabbaka tsarin nan na “Yabawa” da kuma “Ladabtarwa”, wato dukkan wanda aka samu da rashin kyautawa to a ladabtar da shi kana wanda ya kyautata a yaba mishi wannan zai kara taimakawa gwamnatin kana zai kawar da shakku a tsakanin al’umma.

Alh Habibu Kano ya yabawa jami’an tsaron kasarnan bisa irin nasarar da suke samu kan tabbatar da zaman lafiya a wannan kasa tamu kana ya jawo hankalin shugabanni da su kara jajircewa musamman kan harkar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya domin dole sai tsaro ya samu ne yan kasuwar ƙasashen ketare za su shigo kasar su sanya hannun jari wanda hakan zai taimaka wajen habbaka tattalin arzikin kasarnan.

Da ga karshe ya yi addu’ar samun nasara ga gwamnatin Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinibu da sauran gwamnonin kasarnan baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here