Home Siyasa Ci-da-zucin ‘yan adawa ne ya kayar da su zaɓe – Buhari

Ci-da-zucin ‘yan adawa ne ya kayar da su zaɓe – Buhari

161
0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi imani ci-da-zuci ne babban abin da ya janyo taron ‘yan adawar Najeriya suka sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa da ya wuce.

Ya bayyana haka lokacin da ya karɓi gwamnonin jam’iyyarsa ta APC a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Yana cewa a daidai lokacin da jam’iyya mai mulki take aiki tuƙuru don ci gaba da mulki a zaɓukan da aka yi a baya-bayan nan, ‘yan adawa suna can sun cika da ci-da-zuci.

“Sun je suna ta faɗa wa masu goya musu baya a ƙasashen waje cewa, sai sun kayar da APC.

Yayin zaɓen na 25 ga watan Fabrairu, ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu ya smau ƙuri’a 8,794,726.

Sai Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya samu ƙuri’a miliyan 6,984,520.

Ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi yana da ƙuri’a miliyan 6,101,533, yayin da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zo na hudu da ƙuri’a miliyan 1,496,687.

Shugaba Buhari ya ce jam’iyyarsu ta yi nasara ne saboda ta haɗa ƙwarin gwiwar da take shi da taka-tsantsan kuma ta yi aiki tuƙuru har ya kai ta ga nasara.

Ya ce yanzu ma ga shi ci-da-zucin yana haifar wa ‘yan adawan ƙarin matsaloli fiye da kowa.

“Abin na yi musu wahala su yi wa masu goyon bayansu na ƙasashen waje gamsasshen bayani a kan abin da ya sa suka gaza kayar da mu,” in ji Buhari.

A cewarsa, sun haɗa ci-da-zuci da ji-ji-da-kai da bahagon lissafi, kuma su ne suka ja musu faɗuwa a zaɓukan bana. “Wannan ya sake haifar da ƙarin matsaloli a cikinsu. ta kai har ana tambaya. Me ya sa suka kasa kayar da mu?”

Shugaba Buhari ya ce babban dalilin da ya sa shi taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murna kan nasarar da ya samu, shi ne ‘yan adawa sun samu goyon baya, kuma masu goyo musu bayan daga ƙasashen waje sun lasa musu zuma a baki.

“Hakan ta sa sun tafi da burin cewa za su ci zaɓe, za su kayar da mu.

Wanne irin kuskure ne wannan?” shugaban ya sake tambaya.

‘Kaduna zan koma bayan na huta a Daura’

Shugaba Buhari ya kuma yi bayani game da burinsa na rayuwa bayan sauka daga mulki, inda ya ce ya yi niyyar komawa gidansa na Daura, inda zai zauna tsawon wata shida kafin ya koma Kaduna.

Sanarwar Mallam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ƙasar, ta ambato Buhari yana yaba wa “Gwamna Nasir El-Rufa’i na Kaduna saboda ƙoƙarin da ya yi wajen samar da ababen more rayuwa da za su kyautata rayuwarsa da ta al’ummar jihar bayan ya kammala mulki”.

Ƙarin bayani

Tun bayan sanar da sakamakon zaɓen 25 ga watan Fabrairu, masu sharhi kan al’amuran siyasa a Najeriya, suka yi ta tsokaci game da sakamakonsa.

Idan da ‘yan adawan ƙasar sun haɗa ƙarfi wuri ɗaya, mai yiwuwa da cikin sauƙi, sun cinye zaɓen shugaban ƙasa.

Ana dai ɗora alhakin faɗuwar jam’iyyun adawar na Najeriya ne a kan matsalar rarrabuwar kai, da shiga zaɓe a lokacin da suke fama da ɓaraka.

‘Yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen watan Fabrairu guda biyu, Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso, duk sun ɓalle ne daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wadda ta shiga zaɓen kuma tana fama da ɓaraka da rikicin cikin gida.

Idan an haɗa lissafin ƙuri’un da ‘yan takarar biyu suka samu da na jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar jimillar ƙuri’un za su kai 14,582,740.

Adadin dai ya kusa ninka abin da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya samu, har suka ba shi nasara. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here