Home Uncategorized Chinhanci Da Rashawa: Fitattun Mata 5 Da Su Ka Yi Shura

Chinhanci Da Rashawa: Fitattun Mata 5 Da Su Ka Yi Shura

158
0
IMG 20240106 WA0062

Najeriya ta yi ƙaurin suna a wajen cin hanci da rashawa a duniya, lamarin da yake dakushe kima da martabar ƙasar a idon sauran manyan ƙasashe.

A baya, wani lokaci yayin taro a kan yaƙi da rashawa a duniya, an ambato tsohon firaministan Birtaniya, David Cameron na cewa ‘Najeriya ƙasa ce da ta gawurta wajen cin hanci da rashawa’.

Ko a alƙaluman ayyukan rashawa na shekara-shekara, da ƙungiyar Transparency International ke fitarwa, Najeriya na gaba-gaba a duniya cikin jerin ƙasashen da cin hanci ya yi wa katutu.

Masu riƙe da muƙaman siyasar Najeriya, na cikin waɗanda ake zargi da ɗaure wa cin hanci da rashawa gindin zama a ƙasar.

Saboda da zarar mutum ya samu wata kujerar gwamnati, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci za a ga rayuwarsa ta canza saboda irin handama da babakere da kuma almundahanar da ake zargin su ne dalilan da ke sanya su yin rayuwar fiye da albashin da suke ɗauka.

A cikin ‘yan kwanankin nan, akwai wasu manyan ‘yan siyasa mata da suka rasa kujerunsu na gwamnati saboda zargin sun tafka rashawa, inda gwamnati ta dakatar da su domin gudanar da bincike a kan lamarin.

A makon da ya gabata, an fara da dakatar da shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta ƙasa NSIPA, Halima Shehu, sai kuma a ranar Litinin, aka dakatar da ministar ta jin ƙai da yaƙi da talauci, Betta Edu.

Ga jerin waɗansu mata biyar da ake bincike a kansu game da zargin cin hanci da rashawa a Najeriya

Najeriya:

Stella Oduah

Ita ce tsohuwar ministar harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya, zamanin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.

Stella Oduah ta shafe shekaru da dama tana fuskantar shari’a saboda zargin cin hanci da rashawa inda aka sauke ta daga kan kujerarta a shekara ta 2014.

Jonathan ya cire ta daga mukamin minista ne bayan matsin lamba, inda ake zargin ta karkatar da dukiyar da ta kai kusan naira biliyan biyar.

Daga cikin zarge-zargen da ake yi mata har da batun sayen motoci ba bisa ƙa’ida ba.

Har yanzu tana fuskantar shari’a amma dai Oduah ɗin ta musanta aikata ba daidai ba.

Diezani-Alison Madueke

Diezani-Alison Madueke na cikin ministoci mafi ƙarfin faɗa-a-ji a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.

Tun daga shekara ta 2015 da gwamnatin Muhammadu Buhari ta hau kan mulki har zuwa saukatar a 2023, ake yi wa Diezani shari’ar cin hanci da rashawa.

A watan Agusta ne, hukumar yaƙi da manyan laifuka a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar ministar man fetur ɗin ta Najeriya a kotu, kan laifukan cin hanci.

Ana zargin Diezani Alison-Madueke da karɓar cin hancin miliyoyi barkatai na fam ɗin Ingila daga kwangilolin man fetur da iskar gas, da ta bayar don samun cin hanci.

Tun bayan kamun da aka yi mata na farko a London cikin watan Oktoban 2015, Diezani Alison-Madueke take ci gaba da zama a matsayin beli.

Tsohuwar ministar ta musanta zargin.

Sadiya Umar Farouk

  1. IMG 20231226 WA0030

Tsohuwar ministar jin ƙai a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq ta miƙa kanta ga hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC domin amsa tambayoyi a ranar Litinin ɗin da ta wuce.

Tsohuwar ministar ta ce ta amsa gayyatar da EFCC ta yi mata ne domin warware waɗansu batutuwa da hukumar yaƙi da rashawan ke bincike a kai.

A makon da ya gabata ne, EFCC ta gayyaci Sadiya Farouq domin neman bahasi game da zargin almundahanar biliyoyin naira da gwamnati ta ware domin yaƙi da talauci a Najeriya.

Tsohuwar ministar ta musanta aikata ba daidai ba, kuma ta kasance daya daga cikin mafi ƙarfi faɗa-a-ji a gwamnatin Buhari.

Halima Shehu

IMG 20240104 WA0027ò

makon da ya wuce ne, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta ƙasa NSIPA, Halima Shehu.

Ana zargin ta da badaƙala ta biliyoyin naira kuma hukumar EFCC na bincike a kanta.

‘Yan watanni kaɗan da naɗa Halima Shehu a matsayin shugabar NSIPA, shi ne aka samu wannan matsalar har ta kai ga za ta fuskanci bincike.

Halima Shehu dai ta musanta aikata ba daidai ba.

Betta Edu

IMG 20240108 WA0076

Bayan fuskantar matsin lamba na tsawo kwanaki, Shugaba Tinubu ya amince da dakatar da ministarsa ta jin ƙai da yaƙi da talauci Betta Edu nan take daga kan muƙaminta a ranar Litinin.

Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan ministan yaɗa labaran ƙasar ya fitar da sanarwa game da ka-ce-na-cen da ya ɓarke a kan ministar, bayan an zarge ta da tafka jerin almundahana.

Sai dai ta fito tana musanta zarge-zargen waɗanda ta ce bi-ta-ƙulli ne kawai.

Kuma tuni shugaban ya umarci EFCC, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike kan Betta Edu. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here