Home Cinikaiyar Zamani CBN zai hukunta wasu bankuna a Kano kan sabbin kuɗaɗe

CBN zai hukunta wasu bankuna a Kano kan sabbin kuɗaɗe

229
0

Babban bankin Najeriya CBN ya ce zai dauki tsattsauran mataki kan wasu bankuna a Jihar Kano, saboda kin zuwa su karbi sabbin takardun naira da ya samar.

CBN reshen Jihar ta Kano ya jaddada matsayarsa kan cewa cewa karshen watan nan na Janairu zai daina karbar tsaffin kudaden kamar yadda ya sanar tun bara.

Al’umma a fadin Najeriya na ta kokawa kan karancin sabbin kudaden da CBN ya kaddamar a bankuna, baya ga korafin da suke yi na rashin bayar da cikakken wa’adi domin mayar da tsofaffin kudaden bankuna.

Shugaban CBN reshen Jihar Kano Malam Umar Ibrahim Biyu a tattaunawarsa da BBC ya ce, akwai isassun sabbin takardun kudaden bankuna kawai ake jira su je su karba.

“Mun yi magana da bankuna kan cewa su aiko mana da adadin kudin da suke bukata da za a zuba a na’urar ATM domin amfanin yau da gobe ga al’umma.

“Haka muka shaida musu, kuma tuni mun fara bayarwa. Sai dai korafe-korafe sun mana yawa kan ba a samun wadannan kudade a bankuna.

“Wannan dalili ne ya sa muka hau bincike domin tabbatar da cewa suna raba kudaden yadda muka cimma yarjejeniya da su, mun gano wadanda ba sa bayar da sabbin da muka basu,” in ji Malam Umar Biyu.

A cewarsa wasu kuwa na hadawa sabbi da tsofaffi, amma binciken da suka fara gabatarwa ya sanya an samu gagarumin sauyi.

A yanzu idan kaje ATM za ka samu sababbin kudade a kusan ko ina a fadin Jihar Kano.

‘Muna da isassun sababbin kudade amma ban san adadinsu ba’

 

A cewar shugaban bankin reshen jihar Kano tun bayan sanarwar da babban bankin ya fitar, suke bi kasuwanni domin wayar da kan ‘yan kasa domin su gaggauta mayar da tsofaffin da suke da su a hannu ba tare da biyan kudade ba.

“Mun kara jaddada cewa babu wani dalili da zai sa a kara wa’adin da aka tsayar na daina karbar tsofaffin kudi a ranar 31 ga watan Janairun da muke ciki.

Wakilin BBC ya tambayi Malam Umar adadin kudaden da CBN ya aika musu reshen jihar Kano sai ya ce : “Babban bankin ya buga wadannan kudade isassu, ta yadda za su kai ko ina a kasar nan. Yana nan kuma yana ci gaba da bayarwa.

“A gaskiya ba zan iya fada maka adadin kudaden da aka aiko Kano ba da ka, amma an turo yadda ya kamata,” in ji shugaban CBN na Kano.

Ya kara da cewa za su dauki mataki kan duk bankin da bai je ya karbi sabbin kudaden ba.

A ranar Laraba 26 ga watan Oktoba ne Babban Bankin Najeriyar ya sanar da matakin sauya fasalin kudin kasar daga takardar naira 200 zuwa 1000, inda ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.

Kazalika CBN din, ya ce sabbin kudaden da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022, sannan kuma za a ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here