Home Siyasa CBN Ya Sakar Wa INEC Kudaden Gudanar Da Zabe

CBN Ya Sakar Wa INEC Kudaden Gudanar Da Zabe

193
0

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta samu kudaden da ta bukata daga Babban Bankin Najeriya (CBN) domin gudanr da zabubbuka masu zuwa.

Wani Kwamishinan INEC ne ya shaida wa Aminiya hakan ranar Alhamis da dare, kasa da kwana uku kafin babban zaben.

Majiyarmu ta ce an bai wa shugabannin rassan CBN umarnin su bai wa ofisoshin INEC a jihohi kudaden da suke bukata.

Kafin wannan lokaci, akwai fargabar rashin samun kudin a ranar Talata zai haifar wa INEC cikas wajen gudanar harkokinta yadda ya kamata.

INEC ta fuskanci jinkiri wajen samun kudaden ne sakamakon sabbin dokokin da CBN na takaita ta’ammali da tsabar kudi a fadin kasa da kuma sauyin takarun kudi.

Yayin ziyarar da Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya kai wa Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya nuna sun fi bukatar tsabar kudi bisa ga amfani da intanet don su samu damar aiwatar da ayyuka masu yawa.

Ya ce duk da cwea galibi hukumar kan gudanar da hada-dahar kudinta ta intanet ne, amma tana da bukatar tsabar kudi don wasu kebabbun ayyuka.

Ayyukan da ya ce sun hada da biyan motocin haya da za su yi jigilar kayan aiki zusa sassan kasa da magance bukatun ujila da kan taso a ranar zabe da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here