Home Siyasa Buri Na Shine Na Kawo Hadin Kai A Siyasar Jihar Adamawa –...

Buri Na Shine Na Kawo Hadin Kai A Siyasar Jihar Adamawa – Sanata Iya

154
0
Sen. Iya 1

Dan Majalisar Taraiya Mai Wakilatar Adamawa ta Tsakiya, Sanata Aminu Iya Abbas ya yi alkawarin kawo hadin kai wanda ya ce shine kashin bayan kawo cigaba mai dorewa a Jihar.

Sanata Iya ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Majalisar Taraiya a Abuja ranar Talata inda ya ce batum banbanci na siyasa ya kare tunda aka gama zabe yanzu abun da ya rage shi ne neman hadin kan duk masu ruwa da tsaki a siyarsar Jihar Adamawa don kawo cigaba mai dorewa.

“Anyi zabe an gama, yan zu buri na shine kawo hadin kai tsakanin dukkan Yan Jam’iyu a Jihar Adamawa, ba bu batum APC ko PDP maganar anan ita ce me nene zai kawo cigaba. Dukkannin mu Yan Jihar Adamawa ne” Inji Sanata Iya.

Sanatan ya ce akwai rikice rikice na Jam’iyu a Jihar Adamawa wanda hakan ne ya sa ba a fitar da wadanda za su Wakilci Jihar a Mukamin Minista ba sabo da haka ne suke kokarin su ga sun hada kai domin su rinka Magana da murya daya domin kawo cigaba mai dorewa a Jihar.

Sanata Iya ya kara da cewa abun da ya tsara shine duk abun da zai aiwatar a Jihar yana tuntubar dukkan Yan Majalisar Jihar na Taraiya da na Jiha da ke dukkanin jam’iyu domin yaji ra’ayin su domin gudanar da abubuwa da za su kawo cigaba a Jihar ba tare da kawo banbance banbance na jam’iya ba.

Sanatan ya roki yan uwansa Yan Siyasa dama mutanen Jihar Adamawa da su bashi hadin kai wajen ganin an kawo zaman lafia a siyasar Jihar wanda ya ce idan babu hadin kai ba za a samu damar kawo cigaba mai dorewa ba.

Ya yin da yake amsa tambayoyin Yan Jaridu game da yadda ake gudanar da tantance Ministoci, Sanata Aminu Iya Abbas ya nuna gamsuwar da yadda tantacewar take gudana, inda ya ce komai yana tafiya cikin tsari.

Ya ce da zarar sun gama tantance Ministocin za su amince da wadanda suka cancanta domin bawa Shugaban Kasa dama ya kawo cigaban da ya ke da burin kawowa a kasarnan. Sai dai ya ce ya so ace an turo da dukkan sunayen Ministocin a lokaci guda amma haka bata samu ba.

Sanata Iya ya kara da cewa koda ya ke yana daga bangaren Yan Adawa amma ya ji dadin ganin yadda Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bi doka ta hanyar kawo sunayen cikin kwanaki 60 da Tsarin Mulkin Najeriya ya bukata.

Hakan ya ce ya nuna cewa shi dan siyasa ne kuma mai bin doka sabo da haka za su bashi dukkan hadinkai da ya ke nema don ganin ya kawo cigaba da kasarnan ta ke bukata ba tare da la’akari da banbance –banbance da ke tsakanin su ba a Majalisar Taraiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here