Home Siyasa Buhari Ya Sha Alwashin Marawa Shugaba Mai Jiran Gado Baya

Buhari Ya Sha Alwashin Marawa Shugaba Mai Jiran Gado Baya

264
0

Shugaba Buhari na magana ne a taron laccar mika mulki da kwamitin mika mulkin karkashin sakataren gwamnati Boss Mustapha ya shirya.

Shugaban ya ce ya yi amanna wanda zai gaje shi zai dora daga inda ya tsaya kan aiyukan da gwamnatin ta APC ke aiwatarwa.

Shugaban ya godewa kwamitin kula da shirin mika mulkin da aiyukan da ya ke gudanarwa da ya zaiyana da sun yi kyau kwarai.

Taron ya samu halartar tsohon shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, Sultan Muhammad Sa’ad, Bishop Mathew Hassan Kukah da sauran su.

Zabebben mataimakin shugaban Njaeriya Kashim Shettima ya ce ba yadda za a yi a ce gwamnatin Tinubu mai shigowa ta musulunci ce ko fadada lamuran musulunci.

Shttima wanda ke wakiltar Bola Tinubu a laccar mika mulki da aka gudanar a dakin taro na kasa da kasa a Abuja, ya yi tambayar cewa in Tinubu mai son musuluntar da Najeriya ne, me ya sa ya kasa musuluntar da gidan sa wadanda daga kan matar sa duk Kirista ne.

A nan Kashim ya ce an dauke shi ya zama mataimkin ‘dan takara bisa kaddara amma ba wai don batun addini ba kuma zai yi iya kokarin sa wajen yin adalci.

Shettima ya ce lokacin ya na gwamnan jihar Borno an kona wasu majami’u da sauran warare a fitinar Boko Haram amma duk da rinjayen musulmi a jihar ta sa bai hana shi sake gina majami’un ba.

A taron Shettima ya nuna dogaransa wanda ya ke mai bin addinin Kirista ne daga arewa inda babban jami’in tsaron sa Kirista ne kuma ‘dan kabilar Igbo daga Kudu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here