Home Uncategorized Buhari ya amince da jinkirta lokacin ƙidaya a Najeriya

Buhari ya amince da jinkirta lokacin ƙidaya a Najeriya

215
0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da ɗage aikin ƙidayar a ƙasar wanda aka tsara daga ranar 3 zuwa 7 ga watan Mayu.

Yana cewa a bari gwamnati mai zuwa ta sanya lokacin da ya dace.

Amincewar shugaban da wannan mataki, ta zo ne bayan wata tattaunawa da ya yi da mambobin Majalisar Zartaswa ta Tarayya da shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa Nasir Isa Kwarra da ma’aikatansa a Abuja jiya Juma’a.

Ya dai yaba wa ƙoƙarin hukumar kan shirinta na aiwatar da ƙidaya mai tsafta, ta hanyar samar da na’u’rorin zamani da za a yi amfani da su domin aza tubalin ƙidayar da za a dogara da ita a nan gaba.

Muhammadu Buhari ya kuma nusar da cewa an kammala aikin rarraba yankunan da za a ƙidaya da gwajin ƙidaya na farko da na biyu, tare da ɗaukar ma’aikatan wucin gadi da horas da su. Sannan kuma an samo jami’an ayyukan dijital da na’urorin fasahar zamani ta intanet.

Mahalarta taron dai sun gamsu cewa akwai buƙatar gudanar da ƙidayar idan aka yi la’akari da cewa rabon da Najeriya ta yi ƙidaya, shekara 17 kenan, kuma abubuwa da yawa sun sauya, don haka za a buƙaci sake sanin adadin ‘yan Najeriya.

Sanin nasu a cewar zauren taron na fadar shugaban ƙasa, zai taimaka wajen gina duk wani ci gaban ƙasa da zai yi daidai da adadin ‘yan ƙasar da nufin bunƙasa rayuwarsu.

Shugaba Buhari ya umarci Hukumar ta ci gaba da shirye-shiryen da ta fara na ƙidayar 2023, domin kada a watsar da ƙoƙarin da aka faro, ta yadda gwamnati mai zuwa za ta samu bayanan da suka kamata don sauƙaƙa mata cimma burin wannan shiri.

Cikin mahalarta taron, akwai ministan shari’a Abubakar Malami da ministar kudi da tsare-tsare Zainab Ahmed da ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed.

A watan jiya ma, sai da shugaban hukumar ƙidayar jama’a ta Najeriya Nasir Isa Kwarra ya sanar da ɗage aikin sakamakon jinkirta zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi a ƙasar.

Ɗage aikin ƙidayar zai kasance wani babban koma-baya ga Najeriya, ƙasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka.

Sanarwar hukumomi ba ta yi ƙarin haske a kan dalilan da suka janyo dakatar da aikin ƙidayar, kwana huɗu kafin a fara shi ba.

An dai kashe maƙudan kuɗaɗe, kuma an shafe tsawon lokaci ana shirye-shirye don wannan gagarumin da aka ɗage a yanzu.

Babu wani tabbaci a kan takamaiman lokacin gudanar da ƙidayar jama’a ta gaba a Najeriya, duk da yake bisa ƙa’ida kamata ya yi a yi aikin shekara bakwai da ta wuce. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here