Home Siyasa Bola Tinubu: Yadda Mai Nada Sarki Ya Zama Sarki A Najeriya

Bola Tinubu: Yadda Mai Nada Sarki Ya Zama Sarki A Najeriya

182
0

Ranar 1 ga Maris aka bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa mafi ƙalubale tun dawowa mulkin dimokuraɗiyya a 1999.

Nasararsa ta bar baya da ƙura inda manyan ƴan takarar jam’iyyun adawa suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar. Amma ga magoya bayansa, zaɓen ya ƙara tabbatar da gogewar Tinubu a siyasa da kuma shekarun da ya shafe a fagen siyasa.

Masu suka sun nuna damuwa kan lafiyarsa da silar dukiyarsa, kuma suna zargin tsohon gwamnan na Legas da rashawa, zargin da ya musanta.

Mista Tinubu zai fuskanci ƙalubalen tattalin arziƙi da rarrabuwar kan ƴan ƙasa amma magoya bayansa sun ce zai yi amfani da gogewarsa a matsayin tsohon gwamna ya sauya lamurran ƙasar ta Yammacin Afrika

2023

An zaɓi Tinubu ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa bayan ya samu kaso 37 na ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu da ya ja hankali. Akwai tarin ƙalubale gabansa a Najeriya, wadda da ta fi kowace ƙasa yawan jama’a a Afrika; na matsalar tsaro da hauhawan farashi da rashin aikin yi. Mista Tinubu ya yi alƙawalin haɗa kan ƙasar da kuma farfaɗo da tattalin arziki.

2022

Bayan shafe watanni ana raɗe-raɗi, Mista Tinubu ya sanar da ƙudirinsa na takarar shugaban ƙasa. Batun shekarunsa na haihuwa ya mamaye yaƙin neman zaɓensa da zargin rashawa da kuma wanda zai yi masa mataimaki – Musulmi daga arewa – inda masu adawa ke ganin ya saɓa wa al’ada.

2021

Tsohon babban manajan kamfanin Alpha-Beta da ke tattara haraji na jihar Legas Dapo Apara ya taba shigar da ƙara yana zargin Tinubu da yin amfani da kamfanin wajen halasta kuɗin haram da zamba da kuma kauce wa biyan haraji. An zarge shi da mallakar wani ɓangare na kamfanin. Amma bayan shekara ɗaya sun sasanta.

2019

A jajibirin zaɓen shugaban ƙasa, bidiyon wata mota maƙare da kuɗi da ke shiga gidan Tinubu a Legas ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda wasu ke zargin shiri ne na sayen ƙuri’a. An sake zaɓen shugaba Muhammadu Buhari a wa’adi na biyu.

2015

An zaɓi Buhari shugaban ƙasa, wanda ya kawo ƙarshen mulkin shekara 16 na Jam’iyyar PDP. MistaTinubu ya yi alfahari da irin gudumawar da ya bayar wajen samun nasarar a lokacin da ya nemi wannan muƙami a shekarar 2022.

Wani shiri na ‘Zakin Bourdillon’ mai cike da ce-ce-ku-ce wanda aka watsa a kafar talabijin ta AIT ya zargi Tinubu da rashawa da kuma sai abin da ya ce a Leags. Ya nemi diyyar naira miliyan 150 (sama da $325,000) na bacin suna kuma an dakatar da watsa shirin. Daga baya sun sansata tsakaninsu.

2013

Manyan jam’iyyun siyasa huɗu suka kafa jam’iyyar APC domin kawar da jam’iyyar PDP a zaɓen 2015. Mista Tinubu ya yi ruwa da tsaki wajen kafa APC da kuma bayar da goyon baya ga nasarar ɗan takarar jam’iyyar na shugaban ƙasa, Janar Muhammadu Buhari.

2011

Mista Tinubu ya fuskanci kotun ɗa’ar ma’aikata karo na biyu, amma an wanke shi

2007

Mista Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa a matsayin gwamnan Legas, amma daga nan ya zama ‘ubangidan siyasa’ wanda ake zargi ya yin kaka-gida da kuɗaɗen jihar da kuma zaɓen wanda zai zama gwamna.

An fara gurfanar da shi kotun ɗa’ar ma’aikata kan zargin mallakar asusu a ƙasashen waje lokacin da yake gwamna. Ya musanta zarge-zargen.

2003

Tinubu ya sake lashe zaɓen gwamnan Legas. Ana yaba masa wajen haɓaka kuɗaɗen shigar jihar ta hanyar masu saka jari na ƙasashen waje kuma magoya bayansa sun ce ya gyara hanyoyi da ayyukan ci gaban jihar. Masu adawa sun ce abubuwan more rayuwa na cikin mawuyacin hali kuma suna cewa aikin jirgin ƙasa da aka soma tun zamaninsa har yanzu ba a kammala ba tsawon shekara 20.

1999

Najeriya ta dawo mulkin dimokuraɗiyya, An zaɓi Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa yayin da aka zaɓi Mista Tinubu a matsayin gwamnan Legas a inuwar jam’iyyar AD. Obasanjo ya fara mulkar Najeriya a mulkin soja daga Fabrairun 1976 zuwa 1979.

Mulkin Janar Sani Abacha ya kawo ƙarshe bayan ya rasu a watan Yuni. Bayan wata ɗaya Mista Tinubu ya dawo bayan ya tsere.

1994

Galibin masu fafutikar dimokuraɗiyya da magoya bayansu ciki har da Tinubu sun gudu ƙasashen waje don tsoron kama-karyar gwamnatin soji ta Abacha

1993

Najeriya ta faɗa cikin ruɗani bayan soke zaɓen 1993 zamanin mulkin Janar Babangida – wanda galibi ake gani mafi sahihanci da aka taɓa gudanarwa. Bayan ɗan lokaci na gwamnatin riƙon ƙwarya, Janar Sani Abacha ya ƙwace mulki ta hanyar juyin mulki, kuma ana zargin gwamnatinsa da keta haƙƙin ɗan adam da cin hanci da rashawa. Moshood Abiola – wanda ya lashe zaɓen – an ɗaure shi.

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta shigar da ƙorafi a kotu tana zargin alaƙanta asusun Bola Tinubu da hodar bilis tun daga farkon 1988. Ta yi zargin cewa Tinubu ya yi aiki da wanda ake zargi, Abegoyega Akande. Kotun ta tabbatar da tana da dalilin amincewa da cewa kuɗin da ke cikin asusun ajiyar na da alaƙa da safarar ƙwayoyi, amma kuma babu wata tuhuma kan Tinubu. Maimakon haka ya sansanta kuma ya amince ya haƙura da $460,000.

1992

Siyasar Tinubu ta fara ne bayan zaɓensa ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Legas ta yamma ƙarƙashin jam’iyyar SDP. A majalisar ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin kula da bankuna da hada-hadar kuɗaɗe.

1979

Kamar sauran batutuwan da suka shafi tarihinsa, an yi ta bincike sosai a kan tarihin karatun Tinubu a lokacin yaƙin neman zaɓensa, amma Jami’ar Jihar Chicago ta tabbatar da cewa ya yi digiri a fannin nazarin kasuwanci a 1970

Shekarun 1970

Babu cikakkun bayanai game da yarunta da kuma makarantun da Tinubu ya halarta a farko rayuwarsa, amma tabbas ya koma Amurka a tsakiyar shekarun 1970.

1952

Kamar yadda aka wallafa a shafin kamfe ɗinsa, an haifi Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1952 a Legas, Najeriya. Sai dai ƴan adawa da dama suna zargin cewa shekarunsa sun fi haka. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here