Home Siyasa Bola Ahmed Tinubu: Tarihin zaɓaɓɓen Shugaban Najeriya

Bola Ahmed Tinubu: Tarihin zaɓaɓɓen Shugaban Najeriya

257
0

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta sanar da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu na Jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da ƙuri’a miliyan 8,794,726.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana sakamakon zaɓen ranar Laraba bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ne ya zo na biyu a zaɓen da kuri’u miliyan 6,984,520.

Sai kuma dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi wanda ya samu ƙuri’a miliyan 6,101,533.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya zo na huɗu da ƙuri’u miliyan 1,496,687.

Wane ne Bola Ahmed Tinubu?

Bola Ahmed Tinubu, jajirtacce kuma fitaccen ɗan siyasa a Najeriya wanda ke da sarautar Asiwaju a ƙasar Yarabawa, kuma Jagaban a Borgu ta Jihar Neja, ya shahara a fagen siyasa da mulki a Najeriya.

Ana kallon Asiwaju a matsayin wanda ya dade yana jan zarensa tun daga dawowar Najeriya kan mulkin dimokuradiyya a 1999 kuma da alama har yanzu zarensa bai tsinke ba sakamakon irin tasirin da yake da shi a siyasar Najeriya, musamman a kudu maso yamma.

Jama’a da dama na ganinTinubu a matsayin uba a fagen siyasa sakamakon faɗa a ji da yake da shi a siyasar ƙasar Yarabawa da ma Najeriya.

Haka kuma ya kafa mutane da dama a Najeriya inda ya yi musu hanya suka samu muƙamai a tarayya da jihohi.

An haife shi a Jihar Legas, cikin iyalin Tinubu da ya yi fice a jihar.

Ya halarci makarantar firamare ta St. John’s da ke Aroloya da makarantar Children’s Home a Ibadan, da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Daga nan sai ya wuce Kwalejin Richard Daley a Chicago da ke kasar Amurka, bayan samun gurbin yin karatu a Kwalejin.

Daga baya ya zarce zuwa Jami’ar jihar Chicago, a Illinois inda ya kammala ya kuma fito da Digiri a Harkokin Kasuwanci.

Tinubu ya kuma samu kyautar dalibi da yafi kwazo a Jami’ar da kuma shaidar karramawa a bangaren Akanta da Hada-Hadar kudi.

Da zuwansa Amurka a shekarar 1975 da taimakon mahaifiyarsa, matashin mai hazaka, da kuma ke da himmar ganin ya cimma burinsa.

Ya shiga yin ayyuka da za su kawo masa kudi kamar wanke tukwane a gidajen sayar da abinci da aikin gadi da kuma tuka motar-haya domin taimaka masa a bangaren karatunsa.

Baiwar da yake da ita ce ta sa ya shiga jerin dalibai masu hazaka na Kwalejin Richard Daley da kuma ta kai har ya kammala karatu a Jami’ar jihar Chicago a 1979 inda ya fito da digiri a bangaren Kasuwanci.

A shekararsa ta farko a Jami’ar Chicago, an karrama shi da mukamin malami mai taimakawa (tutor), domin taimakon wasu ‘yan uwansa dalibai da ke kananan ajuzuwa.

Ƴan uwansa dalibai da dama sun yaba taimakonsa a bangaren karatunsu wanda har ta kai su ga samun sakamako mai kyau.

A tsawon shekaru da yayi a jami’a, Tinubu ya kasance dalibi mafi hazaka wanda ya yi ta samun kyautar dalibi mai kwazo da kuma shaidar karatu a bangaren Akanta da hada-hadar kudi, inda kuma ya kare digirinsa da sakamako mai daraja ta sama.

A matsayinsa na mai hankoron abubuwa masu kyau da za su zo, Bola ya tsaya tare da yin nasara a takarar shugaban daliban nazarin Akanta da Hada-hadar kudi na jami’ar jihar Chicago a shekarar sa ta karshe.

Aiki da kasuwanci

Kafin kammala karatunsa na digiri, Bola Tinubu ya samu aiki da kamfanin harkar akantanci na Arthur Anderson.

Daga bisani kamfanin Deloitte Haskins (wanda ake kira da deloitte Haskins and Touche a yanzu) suka dauki hayarsa, bayan nan kuma sai ya yi aiki da GTE Service Corporation, wani babban kamfanin sadarwa a kasar Amurka.

A kamfanin Deloitte Haskins and sells, matashi kuma ƙwararre Bola ya fadada kwarewarsa ta hanyar shiga ayyukan dubawa da gudanarwa na General Motors da yin aiki a Babban Bankin Kasa na Chicago da kamfanin Procter and Gamble da International Harvester da General Electric da sauran kamfanoni na Fortune 500.

Bayan ganin kwarewarsa, kamfanin Deloitte sal da yawa ya kan dauki hayar Bola a matsayin jagoran mambobi da ke sa ido a kamfanin.

Bayan dawowarsa Najeriya da kuma samun gogewa a bangaren hada-hadar kudi, Tinubu ya fara aiki da Mobil a matsayin babban mai bincike wanda ta kai har ya zama ma’ajin kamfanin.

A matsayinsa na mutumin da ba ya manta mafararsa da kuma alakarsa da al’umma, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kasance mutumin da ya dauki hidimar al’umma da muhimmanci. Ko da a Mobil, ya jagoranci hidima daban-daban na tara-kudi domin tallafa wa shirye-shiryen ci-gaban al’umma a Jihar Legas.

Ya kuma jagoranci kungiyar Primrose, wata kungiyar siyasa da ke hankoron kawo canji a siyasar Jihar Lagos.

Haka nan, Bola Tinubu ya yanke shawarar shiga aikin hidimar al’umma gadan-gadan ta hanyar ajiye babban matsayi da yake da shi a kamfanin Mobil.

Harkokin siyasa

Shigarsa ta farko fagen siyasa, ya fara ne da shiga sahu wajen kafa jam’iyyar SDP da shi. A shekarar 1992, aka zabe shi a matsayin Sanata da ke wakiltar Yammacin Jihar Legas.

A Majalisar Dattijan Najeriya, ya samu nasarar zama shugaban kwamitin da ke kula da bankuna, kuɗi da kasafi na Majalisar Dattawa – wanda babban kwamiti ne na Majalisar Dattawan Najeriya.

Bayan soke zaben shugaban kasa na ran 12 ga watan Yunin, 1993 da kuma kara wa’adin mulkin soja, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama sahun gaba cikin wadanda suka kafa kungiyar masu rajin kare dimokradiyya da aka fi sani da NADECO.

Sun tunkari gwamnatin mulkin soji na wancan lokaci wajen ganin an kikiro da tsarin dimokuradiyya a Najeriya.

Bola Tinubu ya sha barazana ga rayuwarsa da musgunawa wanda har ta kai ga kamawa tare da tsare shi wanda hakan ya sa ya gudu ya bar kasar.

Duk da haka bai karaya ba a gwagwarmayarsu ta neman tsarin dimokradiyya inda ya zama shugaban kungiyar ta NADECO da ke gudun hijira, inda ya ci gaba da hankoron ganin mulkin dimokradiyya da tsarin shugabanci a Najeriya.

Neman da kungiyar NADECO ke yi daga baya ta sami yin nasara. Yayin da mulkin soja yazo karshe, Bola Tinubu ya dawo Najeriya a shekarar 1998 domin shiga sahun gaba na kawo cigaba da fahimtar juna.

Tinubu ya shiga sahun mutane da suka kafa jam’iyar siyasa mai son ci gaba ta Alliance for Democracy (AD), inda ya samu nasarar zamantowa mai yi wa jam’iyyar takarar kujerar gwamna a jihar Legas.

 

Zama Gwamnan Legas

Bayan samun nasarar zama gwamnan Jihar Legas a zabukan 1999, Tinubu ya jagoranci jihar har na tsawon shekara 8.

Bayan shigar sa ofis a watan Mayun 1999, Bola Tinubu ya jawo hazikan mutane a cikin gwamnatinsa, wanda tare suka tsara kyakkyawan shiri na shugabancin Jihar lagos.

Ajanda 10 da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai sun kunshi bangaren ilimi da lafiya da samar da ayyukan yi da rage talauci, da samar da wutar lantarki da ruwan sha da tsarin zirga-zirga mai kyau da kula da muhalli da doka-da-oda da samar da abinci da kuma farfado da bangaren aikin gwamnati.

Gwamnatin Tinubu, ta inganta tare da gyara tsarin mulki ta hanyar kirkiro da sabbin ma’aikatu irinsu ma’aikatar gidaje da ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa da kuma ta harkokin mata da rage talauci.

A tsawon mulkinsa, Asiwaju Tinubu ya kawo hazikai da kuma kwararru a cikin gwamnatinsa a matsayin kwamishinoni da kuma masu ba shi shawara a bangarori da suka kware.

Ta hanyar tsare-tsare da aiwatarwa, gwamnatin Asiwaju Tinubu ta kara kasafin kudin Jihar Legas daga naira biliyan 14.200 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 240.866 a shekarar 2007 domin Jihar ta samar da karin ababen more rayuwa ga al’ummarta.

Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da kiyaye rabon kasafin kudi na shekara da akalla kashi 60-40 bisa dari a kan kudin da ake kashewa na manyan ayyuka don tabbatar da an samar da ababen more rayuwa ga al’umma.

Asiwaju Tinubu, ta hanyar kirkire-kirkire da sabbin tsare-tsare ya cire Jihar Lagos daga samun kudaden shiga na shekara-shekara na Naira biliyan 14.64 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 60.31 a shekarar 2006. Ya zuwa watan Maris din 2007, jihar ta samu kudin haraji a wata da ya kai naira biliyan 8.2.

Wannan gagarumin kokari da gwamnatinsa ta samu a jihar Lagos ya biyo bayan bijiro da tsare-tsare da kuma aiwatar wa kamar kirkiro da tsarin bankin laturoni da tsarin sa ido a kudaden da ake tarawa da kaddamar da tsarin a na’ura mai kwakwalwa.

Sannan akwai tsarin biyan haraji na laturoni da sake tsara gudanar da ma’aikatar kula da kudaden haraji na jihar da sake fasalta tsarin karbar kudin haraji da samar da bayanan masu biyan haraji.

Jihar Legas karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta zama abin koyi a bangaren tafiyar da aikin gwamnati da kirkire-kirkire da harkokin kudi.

A watan Satumban, 2002, Legas ta kasance jiha ta farko a Najeriya da ta tara kudaden shiga masu yawa don bunkasa ababen more rayuwa.

Jihar ta samu kudade ta hanyar karbo takardun lamuni domin aiwatar da ayyukan ci gaba kamar gyara hanyoyi da gina rukunin gidajen milenia da gina harkokin samar da ruwa da gyara kotuna da samar da wuraren zubar da shara da gina azuzuwa da sauran su.

 

Jajircewar Tinubu

Da taimakon baiwar sa ta siyasa, Bola Tinubu ya hangi barazanar magudin zabe a 2003 daga Jam’iyyar PDP mai Mulki, inda abokansa a yankin kudu-maso-yamma suka saduda da kin yin kamfe na sake zabarsu, amma Tinubu ya bijiro da wani yakin neman zabe mai ma’ana kan irin nasarori da ya samu.

Sauran gwamnonin Jam’iyar AD a jihohin Ondo da Osun da Ekiti da Ogun da kuma Oyo dukkansu sun gamu da cikas wajen sake zabarsu a 2003, a inda jam’iyyar PDP ta samu nasara.

Bola Tinubu ya kasance mutum daya tilo da ya samu nasara a karkashin jam’iyar AD.

Da irin nasarori da ya samu a shugabancin Jihar Lagos, ya samu nasarar kalubalantar gwamnatin tarayya ta fuskar siyasa da kuma shari’a.

Saboda jajircewarsa a wannan lokaci, Bola Tinubu ya kasance mutum daya tilo da ya tsaya tsayin daka wajen hana Najeriya zama kasa mai tsarin jam’iyya daya.

Ya kasance gwamnan jam’iyyar AD daya tilo a cikin jihohi 36 na Najeriya. Duk da haka, bai karaya ba, inda ya shiga sahun gaba wajen karfafa ‘yan siyasa da ke son ci gaba.

A 2007, ‘yan siyasar da ke son ci gaba a kudu-maso-yammacin Najeriya suka dawo da martabarsu.

Don sake zama babban dan siyasa na bangaren adawa, Bola Tinubu ya taka rawa wajen kirkiro da sabuwar jam’iyar ci gaba mai suna Action Congress (AC), wadda daga baya ta koma Action Congress of Najeriya (ACN).

Jajircewar Tinubu ce ta kare Jihar Legas daga mamayar Jam’iyyar PDP, sai dai tsarin da ya bullo da shi ya taimaka masa wajen sake farfado da akidar siyasa wanda daga baya ya dawo da ci gaban shugabanci a fadin kudu maso yamma da kuma Jihar Edo.

Idan za a rubuta tarihin wannan lokaci, Tinubu zai kasance a matsayin mutumin da ya tsaya tsayin daka wajen kawo tsarin siyasar ci gaba a yankin kudu-maso-yamma da kuma Najeriya.

Za a san shi a matsayin mutumin da ya jajirce wajen hana jam’iyar PDP cimma burinta na gudanar da tsarin jam’iyya daya a kusa. Wadanda suke da ra’ayin mulkin dimokuradiyya a Najeriya, tilas ne su jinjina gudummawar da Asiwaju Tinubu ya bayar.

 

Rawar da ya taka wurin kafa APC

A zaɓen 2015, Asiwaju ya zama babban mai goyon bayan hadewar jam’iyyarsa da wasu jam’iyyun adawa biyu – Jam’iyyar CPC da kuma Jam’iyar ANPP domin kawo karshen mulkin Jam’iyar PDP.

Jam’iyyun guda uku sun hade daga baya inda suka samar da jam’iyar All Progressive Congress (APC).

Duba da rawa da ya taka wajen kafa jam’iyyar, an bai wa Tinubu mukamin jagoran jam’iyyar na kasa.

A nan ma, ya sadaukar da burinsa na siyasa, domin karfafa jam’iyyar da ba ta fifiko a kasa baki daya.

A 2015, jam’iyyar ta APC ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2015, wanda karon farko da jam’iyyar adawa ta kada shugaba mai mulki a Najeriya. Tinubu ya taimaka wa Jam’iyyar ta APC wajen samun nasara.

A yau, APCn ita ke mulkin Najeriya bayan samun nasarar zaɓen shugaban kasa. Jam’iyar na kuma da mafi rinjayen mambobi a majalisar tarayyar kasar guda biyu da kuma gwamnoni a jihohi 22 na kasar.

Iyali

Asiwaju Bola Tinubu yana da mata daya mai suna Oluremi Tinubu, wadda sanata ce mai wakiltar Jihar Legas ta tsakiya.

Ta kasance mai fafutikar kare hakkin jama’a da kuma mai ilimi da ake mutuntawa.

Tana kuma gudanar da ayyukan jin kai wadda aka karrama da lambar girmamawa ta kasa ta Officer of the Order of the Niger (OON).

Suna da ‘ya’ya da kuma jikoki (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here