Home Uncategorized Bawa Hafsoshin Tsaro Wa’adi Zai Iya Kawo Karshen Ta’adanci A Yankin Arewa...

Bawa Hafsoshin Tsaro Wa’adi Zai Iya Kawo Karshen Ta’adanci A Yankin Arewa Maso Yamma – In ji Zangon Daura

98
0
Sanata Zangon Daura

An bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya bawa jami’an Tsaro wa’adi na kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa maso yamma wanda hskan na dag a cikin matakai da za a ke ganin za su taimaka wajen ganin an kawo karshen Ta’adanci day a addabi yankin da ma Najeriya baki daya.

 

Dan Majalisar Dattawa mai Wakiltar Katsina ta Arewa Sanata Nasiru Sani Zangon Daura ne ya bukaci hakan a yayin da ya ke wa Yan Jaridu Karin haske akan Kudurin gaggawa da ya gabatar a ranar Alhamis a zauren Majalisar a wani mataki na kawo karshen ta’addanci da ya yiwa yankin na sa katutu.

 

Zangon Daura ya ce Kudurin da y a gabatar wanda an gabatar da irin sa a Majalisar Wakilai jiya Laraba ra’ayi ne na dukkanin yan majalisar jihar Katsina da ma jihohin Zamfara da Sokoto da Kebbi da Nija dama jihar Kaduna wadanda matsalar tsaro ta yiwa kaka gida.

 

Ya ce sun bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya zauna da shugabannin Tsaro da Gwamnoni don sabunta salon yaki da ake yi da ta’aaddaci a kasarnan tun da Salon da ake yi a baya har yanzu ya kasa kawo zaman lafiyar da ake bukata..

 

Sanata Zangon Daura ya kara da cewa dalilin su na dunkulewa don gabatar da kudurin shi ne sun  lura da cewa matakai da ake dauka sun ki yin wani tasiri  da ake bukata shi ya sa suka nemi Majalisar da ta roki shugaban Kasa Bola Tinubu da ya sa ke zama da jami’an Tsaro don sake fito da wani sabon salo na yaki da ta’addanci a jihohi guda shida da ke  Arewa maso Yamma.

 

Sanatan ya kara da cewa har ila yau sun roki shugaban Kasar da ya zauna da Gwamnonin domin su sake tattaunawa da su wajen fito da sabuwar hanyar tun da su ne shugabannin Tsaro a Jihohin na su.

 

Zangon Daura ya yabawa kokarin Gwamnan Jihar sa ta Katsina Dikko Radda wanda ya ce ya sadaukar da rayuwar sa wajen ganin an sami ingantaccen tsaro ta hanyar daukar matakai babu dare babu rana don ganin an kawo karshen matsalar a jihar.

 

Ya ce wannan dalili ne ya sa Yan Majalisar gaba dayan su suka ga cewa ya kamata su marawa kokarin Gwamnan baya ta hanyar gabatar da Kuduri a zaurukan Majalisun Taraiya don jan hankalin Shugaban Kasa da Jami’an Tsaro don ganain an kawo karshen matsalar.

 

Dan Majalisar ya ce sun roki gwamnonin da su yi watsi da batum yin sulhu da Yan’ta’addan sabo da su na da shugabanci daban-daban wanda ya na da wahala a iya yin sulhu da dukkanin kungiyoyin na su.

 

Zangon Daura y a kara da cewa, ko da ya ke yankin da ya ke wakilta akwai saukin matsalar tsaro idan aka kwatanta da sauran yankunan da su ke jihar in da yan ta’addan sun hana jama’a sakat ta hanyar kashe mutane da tashin garuruwa da yiwa mata fyade da hana mutane yin Noma da Kiwa da duk wani nau’I na kasuwanci.

 

Sabo da haka ya roki Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya taimaka wajen ganin ya zauna da Gwamnoni da Hafsoshin Tsaro don sake yiwa salon da akeyin amfani da shi wajen yakin Yan ta’addan don maye shi da wani sabon salo da zai kawo karshen matsalar a yankin na su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here