Home Siyasa Batum Tsaro A Kasarnan: Mun Gaji Da Gafara Sa… Majalisar Dattawa

Batum Tsaro A Kasarnan: Mun Gaji Da Gafara Sa… Majalisar Dattawa

124
0
Senate Chamber

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ta gaji da gafara sa, ga me da batum tsaro da ya addabi Kasarnan tun duk da irin makuden kudi da ake warewa Hafsoshin Tsaro da Alkawaura das u ke yi amma har ya zuwa yanzu batum kullum ba ta canza zani.

Sanata Muhammadu Adamu Aleiro dan Majalisar Taraiya da ke Wakiltal Kebbi ta Tsakiya ya ce dalilin su na ganin Shugaban Kasa Bola Tinubu shi ne domin su tabbatar cewa rahotanni da aka rubuta a baya tun shekara ta 2015 zuwa yanzu wadanda su ka bayar da shawarwari na yadda za a magance matsalar tsaro an yi amfani da su a wani mataki na kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi Kasarnan.

IMG 20240306 182342

Ya ce Majalisar Taraiya ta bawa Jami’an tsaro wadadattun kudade a kasafin kudi da aka gudanar a Majalisa ta tara data goma amma hakan bai sa an sami wani canji na kuzo a gani ba.

Sanata Aleiro ya kara da cewa a kwanakin baya Majalisar Dattawa ta gaiyaci Hafsosin Sojan Kasarnan da duk masu ruwa da tsaki akan harkar tsaro kuma sun tattauna akan batutuwa da dama amma duk da haka ko da jiyama sai da aka kashe sama da mutum 50 a Jihar Benue. Sabo da haka, ba za su zura ido kawai ba su na ganin a na ta kashe Yan Najeriya babu gaira babu dalili.

Ya ce dole a dauki mataki ko a cire Hafsoshin Tsaron  idan ba za su iya ba a canza su da wadanda za su iya ko kuma ayi duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen wannan matsala a Kasarnan.

A wani bangaren kuma Sanata Aleiro ya ce baya goyon bayan amfani da ake yi da Yan Sakai a jihohi domin hakan ya na sanadiyya ra sa rayukan Yan Sakai masu yawa; in da ya ce a Jihar Katsaina an kashe mutum sama da 50. “Ganganci ne ka ce mai Bindigar Toka ya tunkari Mai AK 47 ko AK 49. Tura su kawai ake ye don a kashe su”. In ji shi.

Sanatan ya bayar da shawarar cewa abun yi shi ne Gwamnatin Taraiya ta dauki Karin Jam’an tsaro wadatattu kuma a saya mu su kayan aiki na zamani wandanda su ka yi daidai da barazanar da ake fuskanta domin magance ta.

Ana sa bangaren, Sanata Babangida Hussaini Dan Majalisar Taraiya da ga Jihar Jigawa cewa ya yi sun gaji da tattaunawa akan batum tsaro a Zauren Majalisar Dattawa ba tare wani canji ba shi ne dalilin da ya sa su ka ga dacewar su tunkari Shugaban Kasa tun da shi Chif Sikuriti Ofisa na kasarnan domin lalubo bakin zaren.

IMG 20240306 193418

Sanatan ya kara da cewa Majalisar ta yi nazari na abubuwa da suke da alaka da matsalar tsaro wadanda suka hada da talauci da budaddiyar iyakar kasa, da bangaranci da Siyasa da sauran su wadanda du suna cikin abubuwan da aka duba wajen rubuta wadannan rahotanni kafin a gabatar da shi. Sabo da haka aiwatar da shawarwarin rahoton zai taimaka kwarai wajen maganta matsalar tsaro da ta addabi kasarnan.

Sanata Hussaini ya nuna rashin goyon bayan sa na yadda ake kafa Yan Sakai, in da ya ce horo da ake ba su, bai wadata ba domin mafi karanci horo da ya kamata a ba su shine na shekara guda kuma kamata ya yi ayi amfani da su wajen samar da bayanai ga jami’an tsaro ba a ba su bindiga ba sabo da yin hakan yana da na sa illar.

A daya bangaren ma ya nu na rashin goyon bayan sa na yunkurin da wasu su keyi na kafa Yansandan Jihohi in da ya ce har yanzu Siyasarmu Jaririya ce lura da yadda muke gudanar da ita. Akwai yiwuwar yin amfani da Su wajen cizgunawa abokan adawa da kuma yin abubuwa da basu kamata ba.

Sanatan wanda ya ce abu mafi mahimmanci wanda ya ke ganin zai magance matsalar kasarnan ita ce saka kishin Kasa a zuciyar du ka Yan Najeriya tun daga Firamare wanda idan akwai Kishin Kasa wasu abubuwan ma ba za a aikata su ba sabo da kishi. Sabo da haka akwai bukatar a wayar da kan Yan Najeriya akan Kishin Kasa.

In da ya bayar da misali da yadda abun ya ke lokacin suna Yara yadda tun da ga Firamare ake raba mu su tutur Najeriya musamman wajen bikin Yancin Kai da sauran su. Har ila yau, ya ce a kasashe irin su Amurka ma za ka ga kowanne kofar gida akwai tutar kasar da kuma fito da tsare-tsare da za su saka kishin kasa a zuciyar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here