Home Siyasa Ban yi nadamar bayyana Binani a matsayin gwamna ba – Hudu Ari

Ban yi nadamar bayyana Binani a matsayin gwamna ba – Hudu Ari

197
0

Kwamishinan Hukumar Zaɓe mai Zaman kanta a jihar Adamawa, wanda aka dakatar, ya ce bai yi nadamar bayyana Ai’sha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar ba a zaɓen gwamna na 2023.

Ari ya faɗi haka ne a wata tattaunawa da BBC, inda ya ce ya bi duk dokar da ta dace kafin ayyana ƴar takarar gwamnan ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta yi nasara.

Matakin da kwamishinan zaɓen na jihar Adamawa ya ɗauka a lokacin zaɓen na jihar Adamawa ya janyo ruɗani, bayan da ya bayyana Binani a matsayin wadda ta yi nasara duk kuwa da cewa ba a kammala tattara sakamakon zaɓen ba.

Lamarin ya sanya Hukumar Zaɓe ta INEC ta dakatar da Ari, yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin yin bincike a kan shi da kuma jami’an tsaron da suka ba shi kariya a lokacin da abin ya faru.

A tattaunawar tasa da BBC, Ari ya ce “ni na gaya maka babu nadama, abin da za ka yi bisa doka da oda ai babu nadama.”

Haka nan kuma, Barista Hudu Ari ya musanta zargin da ake yi cewa ya karɓi cin hanci na Naira biliyan biyu domin ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasara a zaɓen.

Binani dai ita ce ƴar takarar gwamna ta jam’iyyar APC a jihar Adamawa a zaɓen 2023.

Ta kalubalanci gwamna mai ci na jam’iyar PDP, Ahmadu Umaru Fintiri wanda a ƙarshe hukumar zaɓen ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen a wa’adi na biyu.

Barrister Hudu Yunusa, wanda rundunar ƴan sanda ke nema, ya ce doka ce ta ba shi hurumin sanar da sakamakon.

Ya ƙara da cewa a shirye yake ya miƙa kansa ga rundunar ƴan sandan Najeriya da ke neman sa nan ba da jimawa ba.

Za ku iya kallon bidiyon tattaunawar a ɓangaren bidiyo na shafinmu da kuma shafukanmu na sada zumunta.

Kiraye-kirayen yin bincike

Ɓangarori da dama a Najeriya sun yi ta kiraye-kirayen a yi bincike.

Kuma a gurfanar da duk wani jami’i da aka samu da hannu wajen aikata ba daidai ba, a zaɓen gwamnan na jihar Adamawa a gaban shari’a.

Cikin masu waɗannan kiraye-kiraye har da zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannunsa ranar Laraba, Tinubu ya buƙaci ‘yan sanda su gudanar da cikakken bincike.

Kuma su bankaɗo duk abubuwan da suka faru a zaɓen cike-giɓi na gwamna a jihar Adamawa da kuma taƙaddamar da ta biyo baya.

Ya yi kira ga waɗanda zaɓen ya ɓata wa rai, su bi kadi ta halastacciyar hanya don ganin an share musu hawaye.

Ya ƙara da cewa a tsarin dimokɗiyya, mutum ɗaya kawai yakan kasance mai nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here