Home Siyasa Ban yi katsalandan a zabukan da suka gabata ba — Buhari

Ban yi katsalandan a zabukan da suka gabata ba — Buhari

188
0

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya yi matuƙar gamsuwa da irin rawar da ya taka a zaɓukan ƙasar da suka gabata, ta hanyar ƙin yin wani katsalandan ko tsoma baki.

Shugaban mai barin gado ya ce ɗokin da ‘yan Najeriya suka nuna wajen zaɓa wa kansu mutanen da za su shugabance su ba tare da wani ya tsoma musu baki ba, manuniya cewa lallai dimokraɗiyyar Najeriya ta kawo ƙarfi.

Cikin wata tattauna da BBC ta yi da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya ce ya ji dadi matuka saboda ‘yan Najeriya sun zabi abin da rans uke so.

Ya ce su ‘yan Najeriya idan har an ba su dama su zabi abin da suke so ba tare da an ce ga abin da zasu zaba ba, to suna zaben abin da suke so ne.

Muhammadu Buhari ya ce,” Da dama daga cikin wadanda suka fadi zaben har da gwamnoni, abin da ciwo babu dadi ba kuma murna ya ke ba, amma kuma manuniyace cewa ‘yan Najeriya su suka san abin da suke so.”

Malam Garba Shehu, ya ce shugaban Najeriyar ya ce duk irin hasashen da aka yi cewa za a samu rikici a wasu jihohi bayan zaben, babu abin da aka yi, wannan ba karamin abin jin dadi bane.

Ya kuma ce, “ Ita gwamnati a yanzu ta samu gamsuwa cewa dukkan wadanda suka fadi zabe babu wanda y ace azo ayi zanga zangar ko a tayar da hankali.”

Mai Magana da yawun shugaban kasar, ya ce ba a taba yin zabe mai tsafta irin wadannan guda biyun da aka yi ba a Najeriya.

Ya ce babban farin cikin shugaban kasar shi ne al’ummar kasarsa sun zabi abin da suke so kuma ba a hanasu su yi hakan ba.

Malam Garba Shehu ya ce faduwar wasu a zaben ta yi wa shugaba Buhari ciwon gaske, to amma kuma ya ce dole ne a girmama duk wani dan Najeriya a bashi hakkinsa. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here