Home Siyasa Ban Ce Ga Wanda Na Ke So Ya Gaje Ni Ba –...

Ban Ce Ga Wanda Na Ke So Ya Gaje Ni Ba – Gbajabiamila

183
0

A wani sakon Twitter da ya fitar, Gbajabiamila ya kore wani rahoto da aka buga a wata jarida wanda ke cewa yana adawa da takarar Mataimakin Kakakin Majalisar Ahmed Idris Wase wanda ke neman a zabe shi a majalisa ta 10.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya jaddada matsayarsa inda ya ce shi har yanzu bai nuna wanda yake so ya gaje shi ba.

A wani sakon Twitter da ya fitar, Gbajabiamila ya kore wani rahoto da aka buga a wata jarida wanda ke cewa yana adawa da takarar Mataimakin Kakakin Majalisar Ahmed Idris Wase wanda ke neman a zabe shi a majalisa ta 10.

Rahoton jaridar ya nuna cewa, Gbajabiamila, na goyon bayan Tajudeen Abbas wanda ya fito daga Zaria a jihar Kaduna.

Sai dai a sakon Twitter, Gbajabiamila, ya ce har yanzu bai bayyana goyon bayansa ga dukkan ‘yan takarar da suka nuna sha’awar su gaje shi ba.

“Ba bayyana goyon bayana ga wani abokin aikina ba” Sakon ya ce.

Shi dai Gbajabiamila, shi ake hasashen zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai nada a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya idan ya kafa gwamnati. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here