Home Siyasa Babu wata tattaunawa tsakaninmu da PDP — NNPP

Babu wata tattaunawa tsakaninmu da PDP — NNPP

191
0

Jam’iyyar hamayya ta NNPP a Najeriya, ta ce babu wata tattaunawa tsakanin dan takararta na shugaban ƙasar, Injiniya Rabi’u Musa Kawankwaso da takwaransa na PDP Atiku Abubakar.

A wata hira da BBC, Atiku Abubakar, ya yi iƙirarin cewa suna magana da wasu jam’iyyun adawa don haɗa-gwiwa su ƙwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Shugaban jam’iyyar NNPP ta ƙasa, Farfesa Rufai Alƙali, ya shaida wa BBC cewa babu wata magana mai kama da haka sam.

Ya ce, “Mu gaskiya ba mu san wannan magana ba haka kuma ba mu san inda ta samo asali ba, mutanenmu sun fusata matuka saboda an sha wahala wajen gina wannan jam’iyya ta mu ta NNPP.”

Ba ma bacci ba ma hutawa muna neman yadda zamu ceto kasarmu, a yanzu jam’iyyarmu na kara samun farin jini da karbuwa a wajen jama’a, in ji shi.

Farfesa Rufa’i Alkali, ya ce,” Idan kana neman jama’a kaje ka nemi jama’a mana, amma baka nemi jama’a kana jira sai an gina jam’iyya sai a dauka a mika maka, ai wannan sam ba haka ake yi ba.”

Ya ce, ‘’Muna gani kowa ya yi nasa mulki na Allah ne.’’

Shugaban jam’iyyar ta NNPP, ya ce ba yadda za a hada mai shekara 66 da mai shekara 78, don haka su abin da suke gani idan ma akwai wanda ya kamata a barwa wannan takara shi ne Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, saboda yana da jini a jika ga kuma kishin kasa.

Ya ce, ‘’ Ita siyasa tana da tsari, don haka idan aka bi tsarin da ya kamata komai zai tafi dai-dai, idan kuwa ba a bi tsari ba, to ba za a ga dai-dai ba.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here