Home Siyasa Babu Mahalukin Da Ya Isa Ya Hana A Rantsar Da Tinubu –...

Babu Mahalukin Da Ya Isa Ya Hana A Rantsar Da Tinubu – David Umahi

193
0

Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya ce duk duniya babu wanda zai iya hana rantsar da zababben Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

Yana wadannan kalaman ne lokacin da zababben Gwamnan Jihar, Francis Nwifuru, ya ziyarce shi ranar Talata, inda ya ce Tinubun ya tsallake siradai da dama kafin ya sami nasarar.

Yayin ziyarar, Francis ya kuma gabatar da takardar lashe zabensa ga Gwamnan David a fadar gwamnain Jihar da ke Abakaliki.

Ya ce, “Lokacin da na ce muku Tinubu zai ci zabe, ba ku yarda ba. Bari na dada fada muku, duk duniya babu mahalukin da zai iya hana rantsar da shi a watan gobe.

“Dalili kuwa a nan shi ne, lokacin da za a iya dakatar da shi, sai Allah Ya ce shi ne. Tun da kuwa Allah Ya ce shi ne, babu wanda ya isa ya ce ba haka ba.”

Gwamna Umahi, wanda kuma ya lashe zaben kujerar Sanata a watan Fabrairun da ya gabata, yanzu haka yana zawarcin kujerar Shugaban Majalisar Dattawa ta 10.

Ya kuma shaida wa bakin nasa cewa ya yi mafarkin ya zama Shugaban majalisar tun tuni. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here