Home Uncategorized Babban Bankin Najeriya CBN Ya Rufe Wasu Bankuna 754 A Fadin Kasar

Babban Bankin Najeriya CBN Ya Rufe Wasu Bankuna 754 A Fadin Kasar

252
0
CBN

Rahotanni daga Najeriya na bayanin cewa, babban bankin kasar, wato Central Bank Of Nigeria (CBN), ya rufe bankuna guda 754 da suka hada da manya da matsakaita da kuma bankunan sayen gidaje a fadin kasar, sakamakon matsalolin da bankunan suka shiga.

Sai dai kuma hukumar kula da bankuna da sanya ido da kuma bada kariya ta hanyar Inshora da ake kira Nigeria Deposit Insurance Corporation NDIC, ta ce ta biya biliyoyin Naira ga mutanen da kudadensu su ka makale sanadiyyar rufe bankunan.

Aminu Hamisu, mataimakin manajan hukumar NDIC na shiyyar Bauchi, a tattunawar Muryar Amurka da shi ya fayyace cewa irin bankunan da rufewar ta shafa.

Ganin cewa, a jiya ne aka kaddamar da bikin ranar ajiya a bankin a Duniya domin wayar da kan jama’a da kuma gabatar da kasidu a wuraren da aka gudanar da tarurruka don fadakar da mutane muhimmancin yin ajiya a bankin, an ji daga Ajiya Bah Zarma, konturola na hukumar NDIC dake shiyyar Bauchi, akan ko ‘yan Najeriya suna da azamar yin ajiya a bankin.

A daya gefen kuma an ji tabakin wassu ‘yan Najeriya kan batun ajiyar kudi a bankuna, da ra’ayoyinsu game da rufe bankunan.

Taken ranar yin ajiya a bankin na wannan shekarar, shi ne ka nemi galaba akan yau dinka domin raya gobe.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here