Home Siyasa Ba Zan Iya Zubar Da Jinin Dan Nijeriya Saboda Muradin Siyasata Ba...

Ba Zan Iya Zubar Da Jinin Dan Nijeriya Saboda Muradin Siyasata Ba —Atiku

205
0

Yayin da ya rage kwanaki hudu a gudanar da zaben shugaban kasa na 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce burinsa na siyasa bai cancanci zubar sa jinin kowane dan Nijeriya ba.

Atiku ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar PDP Jihar Ribas a Abuja, sakamakon dakatar da yakin neman zabensa da ya yi a jihar.

Ya bayyana cewa an dakatar da taron a jihar Ribas ne domin kare rayukan jama’a da gudun zubar da jinin mutane.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya yi alkawarin sanya mata da matasa a cikin shirinsa na farfado da tattalin arziki idan an zabe shi.

Atiku ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki na jihar tabbacin kammala aikin layin dogo na Fatakwal zuwa Maiduguri da kuma tashar ruwa mai zurfi ta Bonny.

 

A cewar Atiku: “ Kwamitin yakin neman zabenmu da kuma jam’iyyar PDP sun amince da cewa babu wani buri na siyasa da ya kai jinin kowane dan Nijeriya.

“Layin jirgin da ba a kammala ba daga tashar Onne zuwa tashar jirgin kasa ta Fatakwal da Maiduguri, zan kammala shi cikin gaggawa da zarar na lashe zabe,” in ji shi. (Leadership Hausa)

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here