Home Ilimi Ba ma goyon bayan shirin gwamnati na bai wa jami’o’i cin gashin-kai...

Ba ma goyon bayan shirin gwamnati na bai wa jami’o’i cin gashin-kai – ASUU

166
0
Asuu President

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU ta ce ba za ta goyi bayan shirin gwamnatin tarayyar ƙasar na bai wa jami`o`i da manyan makarantu `yancin cin gashin-kai ba.

A wannan makon ne Ministan Ilimin ƙasar Farfesa Tahir Mamman, ya ce gwamnatin tarayyar na shirin fito da wasu sabbin hanyoyi ta yadda jami’o’i da manyan makarantun gwamnati za su dinga cin gashin kansu.

Ƙungiyar malaman jami’o’in ta ce irin cin gashin-kan da gwamnatin tarayyar ke tunani ba zai kasance alheri ba ga ‘yan Najeriya.

A tattaunawarsa da BBC, shugaban shiyyar Kano ta ƙungiyar, Farfesa Abdulkadir Muhammad, ya ce, abin da gwamnatin take son yi a yanzu ya saɓa da wanda suke hanƙoron a yi.

Ya ƙara da cewa, matakin na nuna cewa gwamnati tana son ta kauce daga nauyin da ta ɗora wa kanta ne domin a cewarsa jami’o’in ai na gwamnatin tarayya ne ba na wani ba.

‘Matakin ba shi da alaƙa da tsarinmu’

To amma ganin cewa bayar da ‘yancin cin gashin-kai ga jami’o’in gwamnatin tarayyar abu ne da ASUU ta daɗe tana nema sai kuma yanzu ga shi gwamnatin tana son yin hakan sai malamin ya ce wannan ba irin tsarin da suke fafutuka a kai ba ne.

Ya ce : ‘’Yancin da muke magana a kai ba shi suke magana ba.’’

Abin da ƙungiyar ASUU take buƙata shi ne misali gwamnati ta tsame kanta a kan yadda ake zaɓen shugabanni da yin dokokin da suke ganin ba su dace da tafiyar da jami’a ba.

Farfesan ya kuma bayar da ƙarin misali kan yadda ya ce gwamnati za ta kawo wasu dokoki da suka shafi sauran ma’aikata a ce za a yi amfani da su a kan malamai ko ma’aikatan jami’o’i.

A nan malamin ya bayar da misalin tsarin biyan albashi na IPPIS, inda ya ce wata kotu a ƙasar ta yi hukunci da cewa bai dace a yi amfani da wannan manhaja a tsarin jami’o’i ba.

Ya ce, ” amma a maganar bayar da kuɗaɗen tafiyar da jami’a, gwamnati ta ce ba za ta bayar ba, to wane ne zai bayar tun da jami’o’in nata ne mallakarta to matsalar ita ce wane ne zai bayar da kudaden?’’

‘’Idan aka ce jami’o’i su za su nemo kuɗin da za su tafiyar da kansu to ana gaya wa mutane ke nan cewa su shirya, ‘ya’yansu ko kuma su za su nemo waɗannan kuɗaɗe,’’ in ji malamin.

‘Barazanar za ta koma kan ɗalibai’

Masanin ya yi nuni da yadda a baya-bayan nan aka yi ƙarin kuɗin makaranta amma lamarin ya zama abin ƙorafi a Najeriya.

Ya ƙara bayani da cewa, ”idan a kwanan nan yanzu jami’o’in nan suna ƙara kuɗin makaranta daga naira dubu arba’in ya koma dubu 150 ko dubu 200, idan gwamnati ta ce ta daina bayar da ko kwabo a jami’a, ita jami’a ce za ta nemo kuɗin da za ta gina ɗakin karatu da ɗakin bincike da wajen kwanan ɗalibai da biyan albashin ma’aikata da dai duk wasu abubuwa da ake buƙata na tafiyar da jami’a to nawa ke nan za a riƙa cajin ‘ya’yan talakawa da za su zo suna son yin karatu?’’

Malamin jami’ar ya ce, sam-sam ba sa goyon bayan wannan tsari da gwamnatin tarayyar take son ta ɓullo da shi a yanzu, “saboda bai yi mana ba. Tsari ne da zai kawo koma-baya a kan yadda ake tafiyar da ilimi da jami’o’inmu.”

“Saboda yanzu kashi tamanin cikin ɗari na ɗaliban da suke jami’o’inmu idan har aka bari gwamnati ta tabbatar da shi ba za su iya ci gaba da karatu a jami’o’in ba,” in ji shi.

Ya ce su malaman jami’o’i tsarin da suke magana na bayar da ‘yancin cin gashin-kai a makarantun, “ban da maganar cewa su za su nemo kuɗin tafiyar da kansu.”

“Tsarin da har yanzu muke fafutuka a kansa shi ne, wanda jami’a tana da dokokinta na gudanarwa da tafiyar da kanta da kuma zaɓen shugabanninta da kanta, amma ba maganar samar da kuɗaɗen tafiyar da kanta da kanta ba,” a cewar Farfesan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here