Home Siyasa Ba Iri Na Ya Kamata A Tura Majalisar Taraiya Ba – Inji...

Ba Iri Na Ya Kamata A Tura Majalisar Taraiya Ba – Inji Bello Elrufa’i

239
0
Bello Elrufai

Dan Majalisara Wakilai mai Wakiltar Kaduna ta Arewa, Muhammad Bello El-rufa’i  ya ce ba irin su masu kananan shekaru ya kamata a rinka turawa Majalisar Taraiya ba.

Elrufa’I ya fadi haka ne a wata ganawa da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Majalisar Wakilai a birinin Taraiya Abuja ranar Laraba.

Ya ce, Majalisa waje ne dake bukatar mutane da su ke da gogewa kuma su dauki lokaci mai tsawo su na aiki a majalisar. In da ya kara da cewa a kasashen da suka cigaba kamar kasar Amurka Yan Majalisar su mafiyawancin su sun shafe shekaru masu tsawo suna aiki a majalisar.

Har ila yau ya ce, ita majalisa tana bukatar gogewa da ilimi mai zurfi domin yin dokoki da kudure-kudure na kasa suna bukatar mutumin da yake da kwarewa da kuma gogewa a fannoni da yawa.

Sai dai Bello El-rufa’I ya ce a halin yanzu ya himmatu wajen ganin ya fahimci aikin na Majalisa kwarai da gaske kuma ya dauki kwararru da suke kewaye dashi domin su rinka bashi shawarwari da zasu taimaka masa wajen aiwatar da dokoki da kudure – kudure da za su amfani al’umar sa dama kasa baki daya.

“ na fahimci cewa yin doka ko kuduri ya kasu kasha hudu. Misali akwai dokar data shafi Yanki na wato Kaduna North da wadda ta Shafi Jihar Kaduna da wadda ta Shafi Yankin Arewa maso Yamma da kuma doka data shafi Kasa baki daya. Haka na koya kuma haka masu bani shawara za su cigaba da bani shawara wajen yin doka ko kuduri da zai shafi kowanne bangaren da ya dace”.

Game da Kudurin da ya gabatar akan tafiyar wahainiya da aikin titin Kaduna zuwa Abuja da ake gudanarwa ya ce shi ne koda yaushe yana bin titin kuma ana rasa rayuka da dukiya masu yawa sabo da haka ya ga ya kamata a hanzarta a kammala aikin titin kamar yadda aka kusan kammala da ga Kaduna zuwa Kano.

“burina shine na ga an kammala aikin titin Kaduna zuwa Abuja kamar yadda aka kammala da ga Kaduna zuwa Zaria. Tafiya akan titin ya na da mutukar dadi domin babu ramuka ba bu wata barazana”

Hon. Bello Elrufai ya ce acikin kwanaki dari da ya kasance a majalisa ya aiwatar da aiyuka da dama kamar yadda ya dauki alkawari lokacin da ya ke yakin neman a zaben shi. “Lokacin da nake yakin neman zabe na lura da irin halin da mutane suke ciki na matsi na tattalin arziki sabo da haka na fito da tsare tsare don tallafawa jama’a”

Elrufai ya ce ya kafa kwamitoci a bangaren ilimi da lafiya da kuma na tallafawa masu karamin karfi. In da ya zuwa yanzu ya kashe kudade sama da naira miliyan ashirin domin tallafawa al’umma a wadannan bangarori.

A bangaren ilimi ya ce ya fara tallafawa dalibai da ke yankin sa da kudaden makaranta kuma zaici gaba da bayar da wannan tallafi a makarantu da daliban yankin na sa suke. A bangaren lafia ma  ya tallafawa mutane da dama kuma zai ci gaba da tallafawa.

Har ila yau a bangaren bada tallafi ma ya yi tanadi na musamman wajen sayen kayan abinci kuma tuni an fara rabawa ga jama’a, lura da irin halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

Bayan haka, nan ba da dadewa ba zai fito da wani tsari na tallafawa mata masu sana’a da jari na naira dubu dari (N100,000) a tituna daban –daban da ke yankin Kaduna ta Arewa amma burin sa shine duk wacce aka bawa wannan kudi ya zama wajibi ta koyawa wata irin wannan sana’a da ta iya.

“nan ba da dadewa ba zamu fito da wani tsari na rabawa mata naira dubu dari (N100,000) a tituna daban-daban da ke yankin Kaduna ta Arewa. Burin mu shine mu samar da aikin yi ta hanyar bada jari ga mata masu sana’a su kuma su koyar da wata irin wannan sana’a da ta keyi. Ta haka zamu yaki talauci da maganin zaman banza da bunkasa arzikin Jihar”.

Hon. Elrufai, ya godewa mutanen yankin nasa a bisa irin addu’o’I  da suke yi masa da goyan baya da suke bashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here