Home Kwadago Ba gudu ba ja da baya sai mun tsunduma yajin aiki —...

Ba gudu ba ja da baya sai mun tsunduma yajin aiki — NLC

211
0

Bayan da aka gaza cimma matsaya tsakanin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma gwamnatin kasar a kan batun janye tallafin man fetir, NLC ta ce shiga yajin aiki ya zama wajibi.

Kungiyar kwadagon ta dauki wannan mataki ne biyo bayan zaman da ta yi da gwamnatin kasar a daren Lahadi a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

A tattaunawar da BBC ta yi da Kwamared Nasir Kabir, sakataren tsare-tsare na hadaddiyar kungiyar kwadagon ta NLC, bayan ganawar, ya ce basu amfana da komai ba a tattaunawar da suka yi.

“Babu abin da gwamnatin tarayya ta yi a kan sharudan da muka bayar cewa a janye batun cire tallafin mai, don haka tun da gwamnati taki daukar mataki mu kam a bangarenmu ba gudu ba ja da baya sai mun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a fadin Najeriya baki daya” in ji Kwamared Nasir.

Kwamared Nasir Kabir, ya ce “Mun bayar da sharuda kamar na gyara matatun mai ta yadda za a rika samar da mai daga wajensu a kasa, sannan kuma shi kansa tallafin ba a cire shi sai an kawo abin da zai saukakawa mutane hali da za su iya shiga bayan janye shi”.

Ya ce, basu ji dadi ba saboda gwamnatin Najeriya ta dauki matakin janye tallafin mai ba tare da kawo abubuwan da za su saukaka wa ‘yan kasar radadin janye tallafin man ba.

Sakataren tsare tsare na hadaddiyar kungiyar kwadagon ta NLC, ya ce batun cewa nan gaba za a ga alfanun janye tallafin mai a Najeriya, duk zance ne kawai.

“A baya ma anyi haka amma ba abin da aka gani, don haka ko shakka babu a yanzu ma babu wani alfanu da za a gani illa jefa ‘yan Najeriya a cikin mawuyacin hali” in ji shi.

Ya kara da cewa “bisa la’akari da haka mun ba wa gwamnati wa’adi matukar bata dawo da tallafin mai ba, to a ranar Laraba bakwai ga watan Yunin 2023, zamu shiga yaji aiki”.

Kwamared Nasir Kabir, ya ce za su yi wannan yajin aiki ne don nuna fushinsu a kan karin farashin mai da aka yi, wanda kuma duk wani mai kishin Najeriya zai goya musu baya.

A cewarsa, “kowa ya san ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali, sannan kuma azo a kara musu wata ukubar, wannan sam ba daidai bane”.

Tun bayan sanarwar da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi ta cire tallafin man fetur, aka samu karin farashi da kuma fara dogayen layukan mai a sassan kasar.

Hakan ne ya sa kungiyar NLC din ta ce ba za ta amince da wannan halin ba, saboda janye tallafin zai jefa al’umma cikin wahala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here