Home Cinikaiyar Zamani Ba Gaskiya Bane Cewa An Fifita Kudu Kan Arewa Wajen Raba Kasafin...

Ba Gaskiya Bane Cewa An Fifita Kudu Kan Arewa Wajen Raba Kasafin Kudin 2024 – Ndume

200
0
Sen. Ndume 2

Mai  Tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya karyata jita-jita da ke za ga yawa a kafafen sada zumunta cewa an fifita Kuduncin kasarnan akan Arewacin Kasarnan a cikin kasafin Kudi na shekara ta 2024 da aka amince da shi a yau Asabar.

Sanatan ya sanar da haka ne jimkadan da amincewa da kasafin kudin da Majalisar ta yi a wata hira da  ya yi da Yan jaridu a ofishin sa da ke Majalisar Dattawa da ke Abuja.

“ Wani ya turomin da kasafin kudin da ke zagayawa a kafafen sada zumunta wanda da na gani sai da hankali na ya tashi amma da na bi kasafin kudin da aka turo mana na bishi da kyau sai na ga ba haka bane.

Idan kuka lura da labarin da ke zagayawa cewa an bawa kudancin kasarnan mafi tsoka, wanda  da na lissafa du ka kudin sai na ga ya kai tiriliyan N15.9, amma da na duba sai na ga cewa du ka kudaden da aka ware na manyan aiyuka tirilyan N8.7; kun ga da ga wannan bayani, maganar ba gaskiya ba ce”.

Sanata Ndume ya ce a matsayin su na Yan Arewa ba za su zuba ido ba su ga an zalunci Arewa su yi shiru su kyale. In da ya kara da cewa kusan dukkanin wadanda suke da hannu akan raba kasafin kudin Yan Arewa ne.

“Kun ga ni mataimakin Shugaban Kwamitin Kasafin Kudin na Majalisr Dattawa Dan Arewa ne, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Dan Arewa ne, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar  Wakilai, Dan Arewa ne, Ministan Kasafin Kudi Dan Arewa ne, Minista na Noma da ake maganar Ma’aikatar sa,Dan Arewa ne, Mataimakin sa Dan Arewa. To ta ya ya za’ayi wannan rashin adalci mu na gani mu kyale?”

Ndume ya yi alkawarin cewa zai cigaba da bincike kuma a shirye su ke su kare mutumcin Arewa a koda yau she. Sabo da haka ya tabbatarwa da Yan Arewa su kwantar da hankalin su cewa a shirye su ke su ga ba a yi rashin adalci ba a wajen rabon tattalin arzikin Kasarnan ga Arewa.

Sanatan ya kara da cewa dalin su na kara kasafin Kudin da ga Tiriliyan 27.5 zuwa N28.7 shi ne sun lura da wasu bukatu da Shugaban Kasa ya gabatar  mu su wadanda  ba sa cikin kasafin kudin kamar Kidayar Yan Najeriya da za’ayi da bangaren Shari’a sun nemi Karin albashi da kuma dawo da shirin ciyarwa da ake yi a makarantun firamare da kuma kara farashin Dala da sauran su.

Sanata Ndume ya cigaba da cewa bayan haka sun lura da cewa wannan kasafin kudin shine na farko da shugaban kasar ya gabatar ga Majalisar kuma su na so su bashi dama su ga cewa ya cimma kudure-kudure da ya zo da su. Kuma za su sa ido su ga cewa abubuwan da ya ce zai aiwatar da su ya aiwatar da su. Idan bai aiwatar da su ba anan ne za su kalubalance shi.

Mai Tsawarwar na Majalisar ya ce koda ya k e an kawo mu su kasafin Kudin a kurarren lokaci amma sun yi amfani da hikima da kuma na’urorin zamani wajen saukakawa kan su aiki in da su ka rinka yin aiki tare da Yan Majalisar Wakilai a lokaci guda ba dare ba rana domin ganin cewa Kasafin Kudin an amince da shi kafin Karshen Shekara ta 2023 sabo da acigaba da daidaita tsarin kashe kudi da ga watan Janairu zuwa Disamba na kowacce shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here