Home Siyasa Ba bu wani abin dauka a sukar da Obasanjo ya yi wa...

Ba bu wani abin dauka a sukar da Obasanjo ya yi wa demokuradiyya – Fadar shugaban kasa

131
0
Obasanjo

A Najeriya, mahukunta da masana na cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da wani furuci da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi cewa tsarin mulkin demokuradiyyar da aka ara daga kasashen yamma bai yi wa kasashen Afirka rana ba.

Tsohon shugaban Najeriyar ya soki tsarin yana cewa cewa ba ya la`akari da tarihin al`ummar Afirka da matsalolinsu, don haka akwai bukatar a maye shi da wani tsari na musamman.

Wasu dai na ganin cewa bai kamata ya kushe tsarin ba, kasancewar shi ne ya yi uwa da makarbiya wajen mayar da Najeriya kan turbar demokuradiyyar a shekarun baya.

Tsohon shugaban kasar Najeriya, cif Olusegun Obansanjo wanda ya yi furucin a wani taron tattaunawa a kan demokuradiyyar a birnin Abeokuta ya ce tsarin demokuradiyyar da aka ara daga kasashen yama musaman ma Amurka , tsarin demokuradiyyar ne da ya yi hannun riga da matsalolin alummar Afrika saboda ba ya la’akari da tarihin nahiyar da kuma matsalolin alumominta.

Don haka ne tsohon shugaban kasar ya ce ya kamata al’umomin nahiyar su yi karatun ta natsu, su kirkiri wani tsarin mulki da zai dace da nahiyar.

Sai dai ga alama wannan furucin be yi wa wasu dadi ba, ciki kuma har da mahukuta a Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta ce ba bu wani abun dauka a cikin maganar cif Obasanjo saboda a cewarta sai abinda ya ke so ne kadai ke burge shi.

Abdulaziz Abdulaziz mai taimaka wa shugaban Najeriya a harkokin yada labarai:

“ Ai maganar shi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba maganar karba ba ce ba yanzu, duk wata suka da zai yi akan shugabancin Najeriya na wannan lokaci”

“Kowa ya sani cewa Obasanjo duk da cewa ya yi alkaurin ya daina siyasa amma wannan zabe da aka yi na 2023 ya fito ya nuna dan takarar da yake yi , ya nuna jamiyyar da ya ke goyon baya. Don haka wanda yake yana da jam’iyya yana da dan takara kuma aka kada wannan dan takararar na shi. Duk wata magana da zai yi akan shuaabancin da ya ke kai ba za’a karbe shi a matsayin abinda za’a dora a sikelin adalci ba.

Sai dai wasu masana siyasa a Najeriyar na ganin cewa akwai kamshin gaskiya a cikin maganar tsohon shugaban kasar amma ba shi ne ya kamata ya kushe demokuradiyyar ba tunda da shi aka yi uwa da makarbiyya, aka kada aka raya wajan kafa demokuradiyyar a Najeriya.

A dan haka be dace daga baya ya ce kidan ba dadi ba.

Malam Kabir Said Sufi masanin siyasa ne a kwalejin share fagen shiga jami’a ta jihar Kano

“Ba wai abinda ya fada ba ne ba dai-dai ba . Da yake dai shi ne ya fada shi ya sa ake mamaki saboda wasu dalilai”

“A lokacin yana mulkin soja a shekarar 1976 zuwa 1979 suka karbi shawara da kuma daftarin da ya sa aka koma turbar demokuradiyya irin wanda mu ke a kanta halin yanzu.Bayan na Daya, da shi aka karba aka kafa shi”

“Na biyu ya ci moriyarsa ya yi shugaban kasa shekara 8 kuma ba tare da a wancan lokacin ya ga laifin abin ba ko ya soke shi , shi ne kusan abin mamakin”. In ji shi

Masana da dama dai na ganin cewa matsalar shugabanci da ake fama da ita a nahiyar Afrika ba matsalar ce ta tsarin mulki da kasashen nahiyar suka ara suka yafa ba, a ganinsu babbar matsalar ita ce cin hanci da rashawa kuma muddin shugabanni da wadanda ake mulka basu sauya hallayensu ba, to da wuya a ga mai kyau.

Abinda Masana ke cewa kan furucin Obasanjo

Wasu masana siyasa a Najeriya na ganin cewa akwai kamshin gaskiya a cikin maganar tsohon shugaban kasar amma sun ce ba shi ne ya kamata ya kushe demokuradiyyar ba tunda da shi aka yi uwa da makarbiya, aka kada aka raya wajan kafa demokuradiyyar a Najeriya.

A dan haka be dace daga baya ya ce kidan ba dadi ba.

Malam Kabir Said Sufi masanin siyasa ne a kwalejin share fagen shiga jami’a ta jihar Kano

“Ba wai abinda ya fada ba ne ba dai-dai ba . Da yake dai shi ne ya fada shi ya sa ake mamaki saboda wasu dalilai”

“A lokacin yana mulkin soja a shekarar 1976 zuwa 1979 suka karbi shawara da kuma daftarin da ya sa aka koma turbar demokuradiyya irin wanda mu ke a kanta halin yanzu.Bayan na Daya, da shi aka karba aka kafa shi”

“Na biyu ya ci moriyarsa ya yi shugaban kasa shekara 8 kuma ba tare da a wancan lokacin ya ga laifin abin ba ko ya soke shi , shi ne kusan abin mamakin”. In ji shi

Masana da dama dai na ganin cewa matsalar shugabanci da ake fama da ita a nahiyar Afrika ba matsalar ce ta tsarin mulki da kasashen nahiyar suka ara suka yafa ba, a ganinsu babbar matsalar ita ce cin hanci da rashawa kuma muddin shugabanni da wadanda ake mulka basu sauya hallayensu ba, to da wuya a ga mai kyau. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here