Home Siyasa APC ƙyanƙyasar PDP ce don haka ba ma tsoranta – Sule Lamido

APC ƙyanƙyasar PDP ce don haka ba ma tsoranta – Sule Lamido

155
0
Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa da arewacin Najeriya, kuma jigo a jam’iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban riƙon kwarya na jam’iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki ‘yan Najeriya za su sake shiga kunci ba gaskiya ba ne.

Alhaji Sule Lamido ya ce duk ɗan APCn da yake ganin PDP ce ta lalata Najeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali ɗan PDP ne.

Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP masiba ce, annobar bala’ice azaba ce, amma duk da hakan ayi masa afuwa saboda tsoho ne.

Ya kara da cewa; “Amma kar ya manta kuma ‘yan Najeriya kar su manta zaɓukan da aka yi a Najeriya na shekarun 1999 da 2003 da 2007 da 2011 kuri’un PDP kadai sun fi na dukkan jam’iyyu.

Saboda haka, duk dabarar mai dabara, duk wayo mai wayo, sai da aka samu mutanen PDP, da Olusegun Obasanjo a lokacin suna fada da Goodluck Jonathan, da su Bukola Saraki, Atiku da Abdullahi Adamu da Aminu Waziri Tambuwal da sauran gwamnonin PDPn , suka marawa APC baya aka haifi ainahin gwamnatin Buhari.

“Abin da Bisi ya manta shi ne gwamnatin Buhari ‘yar haramun din PDP ce, yar PDP ce amma ta haramtacciya.”

Kan batun da Bisi Akande ya yi cewa ɗan takarar shugaban kasa karkashin jam’yyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da na jam’iyyar Labour Peter Obi na yunkurin haɗewa domin PDP ta sake dawowa kan Mulki domin sake jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Sai Sule Lamido ya kara cewa: “Ai mantawa ya yi cewa sai da aka yi irin yunkurin na haɗewa sannan suka samar da APC kuma duk da ana ganin mu annoba da azaba ne.

Amma aka haifi ‘yar waliyya wato jam’iyyar APC amma gaskiyar magana ita ce jam’iyar APC ‘yar haramun din PDP ce. Saboda ita mace ce da bata haihuwa, sai ‘’yan PDP suka taimaka ma ta akai ciki, dan haka gwamnatin Buhari ‘’yar PDP.”

A karshe Sule Lamido ya ce abin da Bisi ya yi babu laifi, zai iya mantuwa amma ‘yan Najeriya su yi nazari da mulkin PDP da na APC. Shin a yanzu a Najeriyar an fi arziki, ko zumunci ko walwala? A mulkin Buhari na shekara takwas kuma an arewa, an gagara kammala hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wasu dai na ganin tun da jam’iyyar PDP ta rasa mulki, ta gagara taka rawar da ya dace a matsayin ‘yar hammaya domin dawowa karbar iko.

Sai dai Sule Lamidon ya ce duka manyan ‘yan jam’iyyar APC dukka ‘yan PDP ne, “hannun dama ne yake fada da hannun hagu, duk wanda za ka zaga kan ka za ka yi wa”.

“In zagi Abdullahi Adamu, ko Amechi, ko Wamako, ko Saraki, ko Kwankwaso, Ganduje.’’ (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here