Home Siyasa Ana yi wa zaɓen 2023 zagon ƙasa – Tinubu

Ana yi wa zaɓen 2023 zagon ƙasa – Tinubu

207
0

Dan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar APC mai kulkin ƙasar Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin cewar da gangan aka ƙirƙiri batun sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar da batun ƙarancin man fetur domin hana gudanar da zaɓen ƙasar da ke tafe.

Mista Tinubu ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar.

“Ba sa son zaɓen ya gudana. Suna buƙatar hana gudanar da shi. Shin za ku bar su?”, in ji Tinubu a lokacin da yake tambayar dubban magoya bayansa da suka halarci taron gangamin a filin wasa na MKO Abiola a birnin Abeokuta.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi kira ga ‘yan ƙasar za su yi watsi da batun ƙarancin mai, yana mai shawartarsu da su taka ƙafarsu domin jefa ƙuri’arsu a ranar zaɓen.

Ya ƙara da cewa zaɓen ƙasar da ke tafe zai zama gagarumin sauyi ga ƙasar.

“Sun fara zuwa da batun cewa ”babu mai”. Kada wannan ya dame ku, idan babu man fetur, za mu je da ƙafarmu domin jefa ƙuri’armu”.

“Idan kuna so ku ƙara farashin man fetur, ku ɓoye man, ko ku sauya wa takardun kuɗi kala, amma mu za mu ci zaɓe”, in ji Tinubu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here