Home Siyasa Ana yi wa rayuwarmu barazana – Ƴan majalisar Zamfara

Ana yi wa rayuwarmu barazana – Ƴan majalisar Zamfara

135
0
Zamfara state governor

Wasu ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara a Najeriya sun yi zargin cewa ana barazana ga rayuwarsu bayan yunkurin tsige kakakin Majalisar jihar.

A ranar Juma’a ne ƴan majalisar dokokin Zamfara 18 suka sanar da matakin rufe majalisar saboda abin da suka ce “rashin daukar mataki kan halin tsaron da jihar ke ciki.”

“Tun daga daren ranar da muka rufe majalisa aka fara barazana ga rayuwarmu,” kamar yadda Hon Bashir Abubakar Masama ya shaida wa BBC.

Ya ce an kai masu hari a lokacin da suka je wajen ɗaurin aure ranar Asabar, inda aka jikkata wasu daga cikinsu yayin da wasu suka sha da ƙyar.

Hon Masama ya ce an fara nuna su ne, sai daga bisani “wasu ƴanta’adda suka kai muna farmaki aka rufe mu da duka, inda aka yi wa wani mambanmu jina-jina, aka kuma nemi yi masa tsirara, da kyar muka tsira da rayuwarmu.”

Ƴan majalisar sun ce ana yi wa kowane ɓangare barazana, “Kowa ana bugu saboda wanda aka buga a gabana ɗan jam’iyar PDP ne, ni ma kuma PDP nake, amman wanda aka fara bugu ɗan APC ne,” cewar Hon Bashir Masama.

Ƴan majalisar dai sun ce suna tattaunawa kan matakin da ya kamata su ɗauka, musamman hanyar da za su bi domin tseratar da rayuwarsu saboda shi ne mafi mahimmanci a wajensu.

Sun ce suna zargin ɓangaren wadanda matakin da suka ɗauka bai yi wa daɗi ba.

“Muna zargin kodai ɓangaren dakataccen shugaban majalisa ko kuma ɓangaren zartarwa da suke ganin matakin bai yi masu daɗi ba,” in ji Hon Bashir Masama

Hon Shamsudden Hassan wani ɗan majalisar da ya ce ya sha ɗa kyar ya shaida wa BBC cewa “ƴanta’adda kusan 100 aka tura domin halaka su.

“Alhamdulillah mun gano wasu daga cikinsu, sun sanmu kuma mun sansu,” in ji shi.

Martanin gwamnati

Gwamnatin jihar ta ce ba ta da hannu – rikici ne kawai na majalisar kamar yadda kakakin gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris ya shaida wa BBC.

Kakakin gwamnatin ya ce gwamantin ba ta da masaniya kan hari da aka kai wa ƴan majalisar, ” Wannan gwamnatin da ta ke yaƙi da ƴanta’adda, ina za ta kuma aika ɗanta’adda ya kai wa wani hari kuma ta naɗe hannunta, ai ba zai yiyu ba.”

Gwamantin jihar tana gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin majalisar tare da cewa babu wani saɓani da ke tsakanin ɓangaren zartawa da ƴan majalisar.

“Yanzu binciken da ake yi mene ne ya faru domin gano inda gwamnatin za ta shiga a gyara matsalar saboda ba za a so a samu saɓani ta kowane fanni ba.”

Jihar Zamfara dai ta daɗe tana fama da matsalar tsaro ta ƴanbindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa da kuma ɓarayin daji da suka addabi ƙauyukan jihar.

Ƴan Majalisar jiharda suka hada da na APC da na PDP mai mulkin jihar, sun ce sun rufe majalisar ne bayan yunkurin tsige kakakin Majalisar, saboda rashin daukar mataki kan halin tsaron da jihar ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here