Home Labaru masu ratsa Zuciya Ana Ci Gaba Da Gwabza Fada A Birnin Khartoum Na Kasar Sudan

Ana Ci Gaba Da Gwabza Fada A Birnin Khartoum Na Kasar Sudan

189
0

A kasar Sudan an sami rahotan ci gaba da gwabza kazamin fada a birnin Khartoum, babban birnin kasar da kewaye, duk da tsagaita bude wuta na mako guda da bangarorin biyu da ke rikici da juna suka amince.

 

Dakarun Sudan da Dakarun ‘yan sa kai kowanne ya bayyana yana kokarin fatattakar dayan daga tsakiyar birnin Khartoum da kuma yankunan da ke kewaye da fadar shugaban kasa da hedkwatar sojoji.

Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi tir da ci gaba da tashin hankalin. Ya sanya takunkumin hana duk wani dan Sudan da ke kawo cikas ga dimokuradiyya a kasar da ke arewa maso gabashin Afirka gudanar da hada-hadar kudi da ke da alaka da duk wani asusu ko kadarori a Amurka.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira a ranar Laraba da a kawo karshen fadan da ake yi a Sudan da kuma neman goyon bayan kasashen duniya ga al’ummar Sudan, wadanda a cewarsa suna fuskantar matsalokin jin kai.

“Dole ne a ba da agaji a cikin Sudan, kuma muna bukatar cikin gaggawa a samar da damar rarraba agajin ga mutanen da suka fi bukata,” in ji Guterres yayin wani taron manema labarai a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Ma’aikatar lafiya ta Sudan ta ce sama da mutane 500 ne suka mutu sannan kusan 5,000 suka jikkata tun bayan barkewar fadan a ranar 15 ga Afrilu, yayin da ake gwabza fada tsakanin shugabannin sojojin gwamnatin Sudan da dakarun ‘yan sa kai na RSF.

Hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin wannan mako, akalla mutane 334,000 ne fadan ya raba da matsugunansu, baya ga 100,000 da suka tsere daga kasar.

Ita kuma hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa fadan na iya sa sama da mutane 800,000 tserewa daga Sudan. Da yawa suna zuwa kasashe bakwai da ke kan iyaka da Sudan da suka hada da Chadi da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Masar da kuma Habasha. (Muryar Amurka).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here