Home Mai da Iskar Gas Ana biyan sama da naira biliyan 400 duk wata a matsayin kuɗin...

Ana biyan sama da naira biliyan 400 duk wata a matsayin kuɗin tallafin mai – NNPCL

165
0

Kamfanin mai na NNPCL na Najeriya ya ce adadin kuɗin da ake biya a matsayin tallafin man fetur a kowanne wata ya haura naira biliyan 400.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ruwaito shugaban kamfanin Mele Kyari na bayyana haka a Abuja babban birnin ƙasar a lokacin kammala sauya wa kamfanin fuska..

Kyari ya ƙara da cewa kamfanin na NNPCL na kashe kusan naira 202 a matsayin tallafi ga kowacce litar mai a faɗin ƙasar

Ya kuma ce a kowacce rana kamfanin na samar da litar mai miliyan 65 domin wadata ƙasar da man fetur.

Shugaban kamfanin ya ce kamfanin zai ci gaba da yin abin da ya wajaba a kansa na samar wa ‘yan ƙasar man da suke buƙata.

Yana mai cewa biyan sama da naira biliyan 400 a kowane wata a matsayin tallafin man na matuƙar yin tarnaƙi ga harkokin kuɗin kamfanin.

Ya ci gaba da cewa, kamfanin na NNPCL shi ne kaɗai kamfanin da ke shigar da mai cikin ƙasar, kuma zai ci gaba da taka rawa cikin shekaru masu zuwa duk da yawan kuɗin tallafin da yake biya.

Mele Kyari ya ce ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun daina shigar da mai cikin ƙasar sakamakon wahalar da suke fuskanta wajen samun Dalar Amurka da ake buƙata domin shigar da man zuwa ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here