Home Siyasa An Yi Kira Ga APC Ta Yi Taka Tsantsan Wurin Zabo Shugabannin...

An Yi Kira Ga APC Ta Yi Taka Tsantsan Wurin Zabo Shugabannin Majalisun Kasa

180
0

Manyan yan siyasa da kwararru sun mayar da martani akan bayanan da mai magana da yawun Majalisar Dattawa Ajibola Bashiru ya yi cewa akwai matakai da Uwar jamiyyar APC ta kasa za ta dauka wajen shata shiyoyi da shugabanin majalisar dokokin kasa ta 10 za su fito.

Sun kuma bukaci ayi takatsantsan wajen duba cancanta da iya aiki, maimakon sa karfi a batun shiya.

Mai magana da yawun Majlaisar Dattawan Ajibola Bashiru ya ce Uwar Jamiyyar APC za ta zauna bayan azumin watan Ramadan domin ta fito da sifofin da za a yi la’akari da su wajen zabo Shugabanin Majalisar Dattawa da na Wakliai, da suka hada da matsayi, cancanta, iya aiki, addini, da irin gudumawar da shiyoyin suka bayar don nasarar shugaban kasa mai jiran gado.

Bashiru ya ce, a irin wannan lokaci da ake da ‘yan takara da dama musamman daga Jamiyyar APC mai mulki, abu ne mai wuya a ce batun addini ba zai taka rawa ba, duba da batun muslim-muslim da aka yi a kasar.

Bashiru ya ce Shugaban Kasa da mataimakin sa Musulmi ne su, saboda haka za a duba yiwuwar Krista ya shugabanci Majalisar Dattawa. Bashiru ya ce abu ne da dukan manyan kasa za su bada gudumawa wajen ganin an yi abinda ya dace ba tare da an musguna wa wasu ba.

Amma ga tsohon mataimakin shugaban Kungiyar kwadago ta Kasa komred Isa Tijjani, yana ganin bai kamata a duba batun shiya ko addini a Majalisar Kasa ba,

Tijjani ya ce abu ne da mahukunta zasu yi amfani da zurfin tunani na tabbatar da adalci a kasa, saboda Majalisar Kasa Najeriya ce a don haka bai kamata a yi duba ta bangaranci ba.

Tijjani ya ce an taba shugabanci na yan addini daya daga sama har kasa, idan an yi duba da lokacin Mulkin Olusegun Obasanjo. Tijjani ya ce Obasanjo Krista ne, Shugaban Majalisar Dattawa na lokacin shi ne David Mark kuma krista ne shi, mataimakin sa Ike Ekwerenmadu shi ma krista ne, sannan Shugaban Majalisar Wakilai kuma Patricia Ette ita ma Krista ce, kuma an zauna lafiya, har David Mark yayi wa’adi biyu a Majalisar Dattawa. Tijjani ya ce idan akwai fahimta da iya aiki, bai kamata batun banbanci ya kunno kai a majalisar kasa ba.

To sai dai tsohon Ministan Sadarwa Ibrahim Dasuki Nakande ya yi tsokaci akan batun hadin kan kasa inda ya ce Najeriya ta samu matsala a harkar gudanar da mulki, saboda haka mutane na duba batun raba shugabanci shiya shiya a Majalisar kasar domin a samu hadin kan kasa ne.

Dasuki ya ce an kai har mutane na ganin idan wani dan shiyar su yana wuri sai hankalin su ya kwanta. Dasuki yana ganin idan ba a bi shiya shiya ba, zai yi wuya Gwamnati mai shigowa ta iya gina kasa dunkulalliya, aikin ta kawai zai dogara ne kacokan kan yaya za ta hada kan yan kasa, maimakon yin aikin gina ta da kayan more rayuwa.

A yanzu dai, Jamiyyar APC ita ce ta ke da rinjaye a Majalisar Dattawa da kujeru 57, PDP tana da Kujeru 29, LP tana da 6, NNPP ta samu biyu, SDP ta samu biyu APGA da YPP sun samu kujeru daya ko wannen su. A Majalisar Wakilai kuma APC tana da kujeru 162, PDP tana da 102, LP ta na da 34, NNPP na da 18, APGA ta na da 4, SDP tana da 2, ADC tana da 2, sannan YPP ta na da daya. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here