Home Uncategorized An Wargaza Mana Rayuwarmu .. A Cewar Mutanen Gaza

An Wargaza Mana Rayuwarmu .. A Cewar Mutanen Gaza

134
0
Gaza Life after bombing

‘Yan Gaza da rikici ya rutsa da su a inda suke aiki a wasu garuruwa sun shiga cikin zullumi yayin da iyalensu suke kokarin kare kansu daga harin boma-bomai.

A sa’adda aka fara rikici tsakanin Isra’ila da Hamas sama da mako guda da ya gabata, an lalata hanya daya tilo da mutane suke bi su shiga Gaza, sannan ‘yan Filasdinu masu aiki a Isra’ila sun kasa komawa gida ga iyalensu. A halin da ake ciki, maza da dama ne suka makale a Isra’ila yayin da iyayensu, ‘yan uwansu, matansu da yaran su suke kokarin ganin cewa sun tsira daga ruwan boma-boman da a ke yi a Gaza.

Cikin wani gini mallakin karamar hukuma a Ramallah, birnin da ke gabar tekun Maliya, daruruwan magidanta maza ne suke cikin yanayin zullumi yayin da yakin da a ke yi tsakanin Isra’ila da Hamas yake firgita fararen hula a Gaza.

Da dama daga cikinsu sun ce, sun gwammaci hadarin mutuwa da irin labarin da suke ji ta wayar salula ko ta sakon ko ta kwana kan irin wahalhalun da iyalensu suke fuskanta.

‘Yan mazan sun sheda cewa suna neman a sakaye fuskokinsu a bisa dalilan da suka shafi tsaro.

Wani mutum mai suna Saleh Hassan mazaunin Gaza, ya sheda cewa suna gudanar da rayuwar mu ba tare da kula kowaba. Ya ce babu hannun su a wannan rikicin da akeyi. Muna dai kokarin mu gam un rafuwa kan u da iyalen mu asirin mu kawai. Diyata tana shekara na 2 a jami’a inda take nazari akan harshen turanci, zata so a ce ta kammala karatun ta amma kuma yanzu an rusa wannan tunanin. An lalata komai”.

Gaza na da yawan al’umma miliyan 2 dake rayuwa a cikin ta sannan an lalata hanya daya tilo da ta hada garin ta kan iyaka a ranar farko da aka fara rikicin sa’adda Hamas ta kaiwa Isra’ila harin bazata.

Tun bayan nan ne Isra’ila ta ke ta kai hari babu kusan kulum a Gaza.

An sanar da iyalai da suke yankin Gaza su fice daga inda suke wanda yake da nisan akalla kilomita 40 sannan kuma fadinsa ya kai kilomita 10,amma babu hanyar ficewa. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here