Home Siyasa An Shawarci Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Halaye Na Marigayi...

An Shawarci Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Halaye Na Marigayi Na’Abba

165
0
20231229 143117
An shawarci yan siyasa da su yi koyi da halayen irin na Marigayi Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba wanda jajircewar sa ne kashin bayan dorewar Demokradiyya a Kasarnan.

Wannan shawara ta fito ne da ga bakin Sanata mai Wakiltar Takai da Sumaila a Majalisar Taraiya, Sulaiman, Abdulrahman Kawu Sumaila wanda ya nu na alhinin sa game  da rasuwar sa a hirar sa da Yan Jaridu a ofishin sa yau Juma’a a Abuja.
Dan Majalisar Datttawan ya shawarci yan siyasa da Yan Jaridu da  su hada karfi da karfe wuri guda don nemawa kasarnan mafita sabo da talakawa sun dogara da su wajen kawo cigaba mai dorewa.
Sanata Sumaila ya ce, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ya nu na cewa siysar akida ita ce kashin bayan dorewar demokradiyya domin in ba dan ya jajirce ba da ba a samu dorewar siyasa har ya zuwa yanzu.
Sumaila ya kara da cewa rawar da Na’Abba ya taka ita ta bashi kwarin gwiwar tsunduma cikin harkar siyasa wanda ake damawa da su har ya zuwa yanzu.
Dan Majalisar ya kara da cewa Na’Abba mutum ne mai gaskiya da rikon amana kuma jajircecce akan duk abun da ya saka a ga ba wanda ya sadaukar da rayuwar sa domin demokradiyya ta sami gindin zama a kasarnan.
Sanatan ya cigaba da cewa ko an saka sunan Marigayi Na’Abba akan wani abun tarihi a kasarnan ko ba’a saka ba ya rigaya ya rubuta sunan sa da zinare domin  tarihin demokradiyyar kasarnan ba zai cika ba sai  an sa sunan sa.
Sanata Kawu Sumaila ya yi addu’ar Allah ya jikan Ghali Umar Na’Abba ya sa Aljanna Firdaus ta zamo ma sa makoma tare da bawa iyalansa hakuri da juriyar rashin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here