Home Siyasa An Shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu Da Ya Mutumta Tsarin Mulkin Kasar...

An Shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu Da Ya Mutumta Tsarin Mulkin Kasar nan

161
0

An yi kira ga Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya  mutumta Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan tare da Dokokin da ke jagorantar Majalisar Kasa a wani mataki na samar da cigaban Demokradiya mai dorewa a kasarnan.

Zababben Dan Majalisar Taraiya Mai Wakiltar Kano ta Kudu da ga Jam’iyar NNPP, Kawu Sumaila ne ya yi wannan kiran a wani taro na Yan jaridu da ya gudanar a yau Litinin a cibiyar Yan Jaridu da ke Majalisar Dattawa a Abuja.

Kawu Sumaila ya ce, kiran ya zama wajibi ganin yadda wasu masu son su hana ruwa gudu a siyasar Najeriya na kokarin su cusawa Majalisar Kasa Shugabanci na jeka na yika ba tare da la’akari da bin dokoki da suke a Kundin Mulkin Kasar nan ba da Dokoki na Majalisar Kasa ba.

Ya ce, a matsayin Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu wanda gogaggen dan siyasa ne kuma tsohon Sanata toh! bai kamata ya bari wasu su yi masa katsalandan wajen zaben wadanda za su yi aiki tare da shi ba.

Kawu ya ce, kyale Yan Majalisa su zabi wanda su ke so shi ne demokradiyya amma idan aka cu sa wani wanda bai da ce ba to za a sami rashin kyakkyawar dangantaka tsakanin Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Taraiya kamar yadda aka samu a Majalisa ta Takwas da sauran su.

Zababben Sanatan ya yabawa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya Zabi manyan hadiman sa da ga Majalisar Taraiya wato Sanata Gearge Akume,da Sipika Femi Gbajabiamila da Sanata Ibrahim Hadejia.

Ya ce a matsayin sa shima na tsohon Sanata su na da kyakkyawan fata cewa wannan mulki da zai gudanar zai kasance abin alfahari gare su Yan Majalisar Taraiya da ma Yan Najeriya baki daya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here