Home Mulki An Shawarci Shugaba Tinubu Da Ya Yi Amfani Da Makudan Kudade ...

An Shawarci Shugaba Tinubu Da Ya Yi Amfani Da Makudan Kudade Da Su Ke Shigowa Kasarnan Yau, Don Goben Yan Najeriya Ta Yi Kyau

92
0
IMG 20230925 WA0065
An ja hankalin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya yi amfani da makudan Kudade da su ke shigowa kasarnan sakamakon cire tallafin Man Fetur yau don rayuwar Yan Yan Najeriya ta yi kyau gobe.
Dan Majalisar Datttawa mai Wakiltar karamar hukumar Ningi da ga Jihar Bauchi, Sanata Abdul Ningi ne ya bayar da wannan shawara ga shugaban kasar a sakamakon zanga zanga da aka fara a wasu sassan kasarnan wanda ya ce yin hakan ka iya haifar da matsalar da za ta gagari kwandila.
Ya ce Yan Najeriya su na cikin wani hali da ke bukatar mataki na gaggawa wanda in ba haka ba akwai alamu da su ke nunawa cewa Kasarnan za ta iya wargajewa.
“Wannan talauci da yunwa da rashin tabbas na gobe shi ne zai I ya wargaza Kasarnan. Me ne ne wargaza kasa, wannan zanga zanga da a ke yi ni, na yi imanin ba bu  adawa a ciki, tsabar radadin wahala ce a ciki”.
Sanata Ningi ya kara da cewa, shi dan adam idan  cikin sa bai koshi ba, to zai iya daukar duk wani mataki da ya ke gani ya da ce masa. Sa bo da ba wanda zai yarda  ya mutu a tsaye. In da ya ce daukar mataki shi ne, kawai zai farauci kowa. Idan kowa ya farauci kowa, za a sami Kasarnan? Ya tambaya.
Ningi ya ce a bisa wannan dalili ne su ke  Jan hankalin wannan Gwamnati a bisa masaniya da su ke da ita na irin makudan Kudade da su ke shigowa kasarnan. Da a yi amfani da su yau, ba sai gobe ba domin goben Yan Najeriya ta yi kyau. Wadannan kudade ba na ajiya bane, a ceto Yan Najeriya da ga cikin halin da su ka tsinci kan su a ciki.
A wani bangaren kuma, Sanatan Ningi ya yabawa Yunkurin Majalisar Datttawa na tattara dukkannin ma su ruwa da tsaki a kan lamarin tsaro da Majalisar ta yi. “Duk da cewa ina dan adawa amma wannan yunkuri ya nunamin irin jajircewar da Majalisar ta nu na na gaskiya don warware matsalolin da su ke addabar kasarnan”.
Ya tabbatar wa Yan Najeriya cewa ya na da kyakkyawan fatan cewa da gaske a ke wajen magance matsalolin da su ke addabar kasarnan nan da dan lokaci kadan mai zuwa.
In da ya ce a matsayin su na yan Majalisar Taraiya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun saka ido a kan duk abubuwan da a ka ce za a yi don magance matsalar tsaro da matsi na tattalin arzikin Yan Najeriya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here