Home Siyasa An Shawarci Majalisar Taraiya Da Ta Maidawa Hukumar INEC Gudanar Da Zaben...

An Shawarci Majalisar Taraiya Da Ta Maidawa Hukumar INEC Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi

119
0
Hon. Leko 2

An shawarci Majalisar Taraiya da ta maidawa da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa wato INEC damaar gudanar da Zabe na Kananan Hukumomi a wani mataki na kawo gyara a yadda a ke gudanar da zabe da Siyasa a Kasarnan.

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltal Bogoro da Dass da Tafawa Balewa da ga Jihar Bauchi, Hon. Jafaru Gambo Leko ne ya bayar da wannan shawara a lokacin da ya ke yin sharhi game da jawabin Kakakin Majalisar Wakilai, Spika Abbas Tajuddeen a hirar sa da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Abuja.

Hon. Leko ya ce, dama da aka bawa Jihohi na da su rinka gudanar da zaben Kananan Hukumomi ya nu na karara irin koma baya da aka samu wajen gudanar da zaben in da a halin yanzu an daina gudanar da zabe a kananan Hukumomi. In da ya ce nadi kawai ake yi wanda hakan ya kawo koma baya a siyasar kasarnan.

Dan Majalisar ya kara da cewa bawa Jihohi dama da akayi na da su rinka gudanar da zaben kananan Hukumomi ya janyo mutuwar demokaradiyya da ga tushe tare da kawo tabarbarewar al’amura na tattalin arziki da tsaro domin kuwa Kananan Hukumomi su suka fi kusa da jama’a amma son zuciya ya sa an ka she su.

Sabo da haka, ya bukaci da a mayarwa da Hukumar Zabe ta Kasa wato INEC dama na gudanar da zabe a wani mataki na kawo gyara a yadda ake gudanar da siyasa a kasarnan.

Bayan haka, ya kara da cewa ya zama wajibi kasashen waje da su daina yin katsalandan akan harkokin siyasar kasarnan tahanyar bayar da kudade tare da gindaya sharudai wajen yadda za a tafiyar da siyasar Kasarnan wanda ya ce shawarar su ce ta sa aka maida zaben kananan Hukumomi ga Jihohi wanda hakan ya haifar da koma bayan da aka samu a halin yanzu a siyasar kasarnan.

Dangane da matsi na tattalin arziki da a ke fama da shi a kasarnan  Hon. Leko ya ce sai dai a ce Innalillahi wa’inna ilaihir raju’un. Ya ce mutane su koma ga Allah su roki shi da ya kawo sauki domin kuwa abun ya kai lahaula wala kuwata.

Sai dai, ya bayar da shawara da cewa ya na ganin ya kamata a yaki cinhanci da rashawa ta hanyar komawa tsarin da Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya fito da shi na gudanar da “Cashless Policy” wato rage yawon kudi a hannu jama’a wanda shine zai taimaka wajen rage rashawa domin idan aka ce za a yiwa mutum “transfer” ba zai yarda ba domin ya san a na da sheda da za’a iya gabatarwa idan bukatar hakan ta taso.

Ya ce, ko batum satar mutane da a ke yi ya yi sauki lokacin da aka fito da tsarin kashles wanda hakan zai bayar da dama a gano wanda aka turawa kudin cikin sauki tare da kama wadanda suke da hannu akan batum.

Har ila yau, Hon. Leko ya shawarci yan Kasa musamman samari da su daina dogara da cewa sai sun yi aikin gwamnati a maimakon haka su rungumi yin sana’o’I a wani mataki na dogara da kai. Hakan ya ce zai magance rashin aikin yi da bunkasa tattalin arzikin kasarnan baki daya.

Game da batum tsaro da ya ta’azzara a kasarnan, ya ce shawarar da Spika Abbas ya bayar na cewa akwai bukatar a kirawo taro na masu ruwa da tsaki domin su bayar da shawarwari da za su magance matsalar tsaro da ta addabi kasarnan abu ne da ya dace.

Hon. Leko ya kara da cewa Najeriya ta tanadi dokoki masu kyau wajen magance tsaro da sauran batutuwa da suka shafi kasarnan amma babbar matsalar it ace ba a aiwatar da dokokin ta hanyar hukunta duk wadanda aka samu da karya dokar. Sabo da haka ya ce idan ana bukatar magance matsalolin da suka addabi kasarnan akwai bukatar a tsaurara hukunci akan duk wanda aka samu da karya wata doka.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here