Home Uncategorized An kashe mutum goma ‘yan gida ɗaya a wani harin bindiga cikin...

An kashe mutum goma ‘yan gida ɗaya a wani harin bindiga cikin Afirka ta Kudu

181
0

An harbe mutum goma ‘yan gida ɗaya bayan wani rukunin mutane sun kutsa kai gidansu a birnin Pietermaritzburg cikin lardin KwaZulu-Natal a Afirka ta Kudu.

‘Yan sanda sun ce ‘yan bindigar sun shiga gidan ne inda mata bakwai da maza uku suka taru kuma suka buɗe musu wuta.

Babu bayanai a fayyace kan abin da harzuƙa kisan kan.

Ministan ‘yan sanda Bheki Cele da sauran manyan jami’ai daga rundunar ‘yan sandan Afirka ta Kudu sun kai ziyara gidan da aka kai harin.

Wannan ne karo na biyu da ake kashe ɗumbin mutane a KwaZulu-Natal a cikin wannan mako bayan an hallaka mutum huɗu ranar Alhamis a wani gida da ke KwaMashu, arewa da birnin Durban mai tashar ruwa. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here