Home Tsaro An Bukaci Al’umar Dutsin-ma/Kurfi Da Su Bawa Jami’an Tsaro Goyon Baya Don...

An Bukaci Al’umar Dutsin-ma/Kurfi Da Su Bawa Jami’an Tsaro Goyon Baya Don Magance Barazanar Tsaro A Yankin

180
0
HON. Balele 3

An yi kira ga al’umar Dutsin-ma da Kurfi da ke Jihar Katsina da su cigba da bawa jami’an tsaro da gwamnatin Jiha hadin kai da goyon bayan a yunkurin su na ganin an sami tsaro da zaman lafiya a yankin domin samun cigaba mai dorewa.

Dan Majalisar Taraiya mai wakiltar yankin Dutsin-ma da Kurfi a Majalisar Kasa, Hon. Aminu Balale (Dan Arewa) ne ya yi wannan kira a hirar sa da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Hon. Balele ya ce harkar tsaro harka ce da ta shafi kowa da kowa ba tare da la’akari da banbancin jinsi ko siyasa ba sabo da haka akwai bukatar mutane su hada karfi da karfe wajen bawa jamian tsaro da gwamnati goyon baya wajen ganin an kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin.

“Ma su garkuwa da mutane ba sa bambamcewa tsakanin mutum dan APC ne ko PDP kafin su sace shi sabo da haka ya kama mutane su ajiye bambamcin jam’iya a gefe su bawa hukumomi goyon baya domin su magance matsalar tsaro da ta addabi yankin” in ji  Dan Arewa.

Sabo da haka, ya kara da cewa mutane kada su yi kasa a gwiwa wajen ganin sun baiwa hukumomi bayanai da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Dadin dadawa, Hon. Balele ya ce gwamnati da jami’an tsaro su na yin aiki tukuru ba dare ba rana wajen ganin sun kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a yankin.

Ya ce a matsayin sa na Dan Majalisar Taraiya ya san irin kokarin da ake yi na tuntuba da tattaunawa da hukumomin tsaro domin lalubo hanyoyi da za su taimaka wajen ganin an kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da an cutar da su ba.

Hon. Balele, ya ce shi a karan kansa ya rubutawa dukkan jami’an tsaro  da suka hada da shugabannin Yan Sanda da Civil Defence da Sojoji da Jami’an tsaro na farin kaya da sauran su domin su kawo dauki wajen ganin an samar da tsaro da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Dan Majlisar ya yiwa  al’umar yankin albishir cewa nan bada dadewa ba komai zai koma kamar yadda yak e a da na zaman lafiya da kwanciyar hankali. In da ya ce manoma da Yan Kasuwa za su cigaba da harkokin su kamar yadda suka saba nan bada dadewa ba da ikon Allah.

Ya yabawa Gwamnan Jihar Katsina Dr. Dikko Radda game da irin jajircewa da yake yi na tabbatar da tsaro a Jihar ba dare ba rana; inda ya bukaci da ya cigaba da kokarin da ya ke yi har sai an sami ingantaccen tsaro da zaman lafiya a Jihar Katsina baki daya.

A wani bangare kuma, Hon. Dan Arewa ya yi alkawarin cigaba da tallafawa al’umar sa ta hanyar bayar da tallafi a bangaren ilimi da sauran bangarori kamar bayar da Keke Napep 43 da Siyana guda 10 domin tallafawa harkar zirga zirga a yankin na sa a farashi mai rahusa.

Dan Arewa ya roki al’umar ta sa da su cigaba da bashi hadin kai da goyon baya wajen ganin ya kawo musa romon demokradiyya. In da ya yi alkawarin cewa ba zai ba su kunya ba da yardar Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here