Home Siyasa An bayyana zaɓen Adamawa a matsayin wanda bai kammalu ba

An bayyana zaɓen Adamawa a matsayin wanda bai kammalu ba

320
0

Babban jami’in tattarawa da sanar da sakamakon zabe a jihar Adamawa ya bayyana zaben gwamna na jihar da aka yi ranar Asabar a matsayin wanda bai kammala ba.

Jami’in ya bayyana haka ne dazun nan a cibiyar tattara sakamakon zaben bayan da aka sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Fufore da ake ta dako.

Bayan sanar da sakamakon kananan hukumomi 21 na jihar, Ahmad Umar Fintiri na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 421,524.

Yayin da babbar abokiyar hamayyarsa ta Jam’iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani ta samu kuri’u 390,275.

Sai dai baturen zaben ya ki amincewa da sakamakon zaben da aka kawo daga karamar hukumar Fufore inda ya ce an samu banbanci a alkaluman da aka sanar da kuma wanda aka dora a shafin hukumar zabe.

Zaben da aka yi a jihar na daya daga cikin wadanda hankula ya karkata a kai la’akari da cewa wannan ne karon farko da aka samu mace daga arewacin Najeriya da ta tsaya takarar gwamna a jihar Adamawa. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here