Home Diplomasiyya An Amince Za A Shigar Da Kayan Agaji Zuwa Gaza – Biden

An Amince Za A Shigar Da Kayan Agaji Zuwa Gaza – Biden

168
0
Gaza agaji

Shugaba Biden ya ce ya samu nasarar ƙulla wata yarjejeniya da za ta bayar da damar kai agaji Gaza, kwana 12 bayan Isra’ila ta ƙaddamar da luguden wuta da ya jefa jama’a cikin buƙatar tallafi.

Mr. Biden ya bayyana hakan ne a kan hanyar sa ta komawa Amurka bayan gajerar ziyrar da ya kai Isra’ila, inda ya ce shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya amince da buɗe mashigar Rafah don shigar da manyan motoci 20 ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza.

Shugaba Biden ya ce dole ne a yaba wa shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi abisa gudunmuwar sa don ganin an cimma wannan yarjejeniya.

Ya ce ya fito ƙarara ya shaida wa Isra’ilawa cewa akwai buƙatar tallafawa Palaɗinawa fararen hula a daidai lokacin da ake ci gaba da yaƙar Hamas.

Ya ce “Wannan tattaunawa ce ta ƙeƙe da ƙeƙe kuma muna fatan samun kayan tallafi daidai gwragwado. Ina tunanin za a samu manyan motocin ɗaukar kaya 150 ko fiye da haka amma ba dukkan su za a tura Gazar lokaci guda ba.

Za a riƙa shigar da tallafin ne zango zuwa zango kuma wakilan Majalisar Dinkin Duniya ne za su karɓa, su kuma rarraba kayan. Amma fa akwai shaɗin cewa idan Hamas ta nemi ƙwace kayan ko kuma ta kawo cikas ga shigar da su, to wannan yarjejeniya za ta wargaje.‘’

Tun da farko a yayin ziyarar da ya kai birnin Tel Aviv na, Mr Biden ya sanar da cikakken goyon baya ga Isra’ila, amma ya yi kiran yin taka tsan-tsan.

Shugaba Biden ya kuma sanar da tallafin dala miliyan ɗari ga Falasɗinawa.

Ya ce ‘’A yau ina sanar da tallafin dala miliyan ɗari don gudanar da aikin agaji a dukkan ɓangarorin Gaza da kuma gaɓar yamma da kogin Jordan. Wannan kuɗi za su taimaka wajen tallafawa Falasɗinawa fiye da miliyan ɗaya da kuma gudanar da sauran ayyukan gaggawa a Gaza.’’

Isra’ila dai ta ce ba zata hana a kaiwa Gaza tallafi ba ta Masar, kamar yadda Mr Biden ya buƙata.

Ofishin Firaiministan Isara’ila ya ce ana iya shiga da kayan tallafin idan har ba za a miƙa kayan ɗinkin ga Hamas ba. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here