Home Ilimi Amnesty International Ta Yi Kira Ga Al’ummar Najeriya Da Su Daina Horo...

Amnesty International Ta Yi Kira Ga Al’ummar Najeriya Da Su Daina Horo Mai Tsanani Ga KanananYara

233
0
20230622 121001

Kungiyar nan mai Rajin Kare Hakkin Al’umma musamman Kananan Yara da ga cin zarafi wato “Amnesty International”ta yi kira ga Yan Najeriya da su daina yiwa kananan Yara horo mai tsanani a makarantu na Boko da na Islamiyya domin hakan ya na da mummunan illa ga Yaran a rayuwar su.

Shugaban Kungiyar a Najeriya Isa Sanusi ne ya yi wannan kira a wani taro da Kungiyar ta shirya na masu ruwa da tsaki akan harkar ilimi a ranar Alhamis a birinin Taraiya Abuja.

Isa ya ce Kungiyar ta lura cewa cin zarafin kananan yara ya na karuwa a Najeriya shi ya sa ta shirya wannan taro na masu ruwa da tsaki akan harkar ilimi domin lalubo mafita ta yadda za a samu sauki na cin zarafin kananan Yara a Najeria.

“ mun lura cewa cin zarafin kananan Yara da gallaza musu yana karuwa a Najeriya kai harma wani lokacin ana cutar da su inda sukan rasa wani sashe na jikin su. Kai in takaice maka labara wani lokacimma har takan kai ga rasa rayukan su. An sami irin hakan a nan Abuja a wata makaranta a Kwali, da Jihar Legas da safen nan ma na sami wani rahoto na gallazawa ga wani yaro” inji shi.

Isa ya ce dalilin haka ne ya sa suka shirya wannan tattaunawa na masu ruwa da tsaki domin a  lalubu mafita wajen ganin an sami sauki wajen cin zarafin kananan yara a makarantu na sakandare da ma firamare.

Ya ce makarantu gurare ne da ya kamata ace gurare ne da ke da aminci in da duk wanda ya tura dansa makaranta ya aminta cewa ba za a ci zarafi ko musgunawa ga yaron sa ba amma abun ba haka ya ke ba. Sabo da haka ne Kungiyar Amnesty ta ke so ta zaburar da hukumomin da suka dace domin su dauki mataki na ganin an yi horo mai tsanani ga duk wanda aka samu ya ci zarafin karamin yaro a makarantu.

Ya kara da cewa babbar illar da cin zarafin yaro a makarantu zai yi shine na farko ya cirewa yaron sha’awar karatu na biyu kuma ya sa iyaye daina kai ‘yayan su makaranta wanda wadannan zasu haifar da mummunan komabaya a harkar ilimi a Najeriya.

Shugaban ya ce sakamakon wannan bincike na su za su mikawa duk Ministan Ilimi da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada tare da bayar da shawarwari da zasu kawo karshen cin zarafin kananan yara a makarantu na Sakandare da Firamare a Najeriya.

Daya da ga cikin wadanda suka halarci taron wani malamin Makaranta a birnin Taraiya Abuja, Muhammad Kusharki y a tabbatarwar da Jaridar Viewfinder cewa lallai gaskiya ne ana cin zarafin kananan yara a makarantu amma da sauki a birinin Taraiya Abuja idan aka kwatanta da wasu jihohi da kananan hukumomi.

Y ace Ma’aikatar Ilimi ta fito da tsare tsare na kariya kuma ana kokarin dabbaka su a Abuja sabo da haka ne ya sa ba a cika samu matsalolin sosai ba. Amma ya aiyana cewa dalilin ta’azzarar matsalar shine gwabnati ba ta bawa malamai horo da muhimmanci ba.

Kusharki ya ce a baya kafin a tura malami aji sai ya sami cikakken horo tun da ga kwaleji amma yanzu abun ba haka ya ke ba ana daukar malamai da ba harkar koyo da koyarwa suka karanta ba sa bo da haka ba su san irin illar da ke tattare da cinzarafin kananan yara zai haifar ba ga al’umma.

A yayin gabatar da ta sa makalar, Farfesa Bem Angwe ya gabatar da hanyoyi masu yawa daka iya kawo karshen cin zarafin kananan yara. Inda ya ce yara su na da wasu hakkoki akan al’umma kamar yanci na su rayu kamar kowa da yanci na kare su da ga dukkan abun da ka iya cutar da su da kuma yanci na a ba su dama su cimma burinsu na rayuwa.

Ya ce hakan ba zai samu ba sai jama’a sun san hanyoyi da su ka kamata su bi wajen ganin sun bawa yara tarbiyar davta dace da su. Inda ya ba da misali lokacin da ya na dan makarantar sakandare inda Allah ya hore ma sa fahimta na Ilimin lissafi amma kash Malamin sa shi kuma sai bai fahimci baiwar da Allah ya yi ma sa ba inda ya koreshi daga aji wai ya na ganin kamar hazakar sa ya na nuna ta ne don ya kure malamin. Ya ce tun da Malamain ya kore shi da ga aji ya tsani darasin lissafi.

Farfesa Angwe ya yi kira ga jama’a musamman iyaye da malaman makaranta da ako da yau she da su rinka jan yara a jiki suna sauraron su domin fahimtar irin bukatun su da baiwar su da matsalolin su. Da ga karshe ya ja hankalin iyaye da Malamai da su kauracewa yin horo mai tsanani ga kananan yara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here