Home Siyasa Amincewa Shugaba Tinubu Ciyo Bashin $800m, Alfanu Ko Rashin Sa?

Amincewa Shugaba Tinubu Ciyo Bashin $800m, Alfanu Ko Rashin Sa?

164
0

Majalisar Dattawa ta amincewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya ciyo bashin dalar Amurka miliyan 800 don tallafawa Yan Najeriya marasa karfi sakamakon matsi na tattalin arziki.

Majalisar ta amince da wannan kuduri na shugaban kasa bayan da aka tafka mahawara na cancanta ko rashin cancantar ciyo bashi a zamanta na ranar Alhamis.

Har ila yau Majalisar ta amince da yin gyara akan kasafin kudi na 2022 domin ya bayar da dama a samar da N500 Biliyan daga cikin kasafin kudi na N819, 536 don tallafawa Yan Najeriya sakamakon cire tallafin Man Fetur da gwamnatin tayi a watan day a gabata.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya karanta bukatar ta shugaban Kasa a zauren Majalisar wanda ba tare da bata lokacin ba Majalisar ta yi mahawara akan bukatar kuma ta amince da bukatun nasa.

Wadannan Kudade N500 biliyan da aka amince da su za a rabawa yan Najeriya mutum miliyan 12 kowannen su N8,000 har na tsawon watannin 6 kamar yadda takardar fadar shugaban kasar ta nema. Kuma Bankin Duniya ne wato World Bank zai taimakawa Najeriya wajen wannan batum.

Dag a cikin wadannan kudade wato N819,536 biliyan za a bawa Ma’aikatar Noma N19 biliyan da Ma’aikatar Aiyuka da Gidaje za a bata N185 biliyan sai kuma Babban Birnin Taraiya Abuja za a kasha N10 biliyan.

Sen. Hanga

Sanata Rufa’I Hanga Dan Majalisa Mai Wakiltar Kano ta Tsakiya ya yi Karin haske akan batum inda ya ce dalilin amince da ciyo wannan bashi shi ne babu kudi a asusun Gwamnatin Najeriya kuma idan ba su amincewa Shugaban Kasa ya ciyo wannan bashi ba , ba za a samu kudade da za’a tallafawa Yan Najeriya ba a wannan matsatsi da ake ciki.

Sanata Hanga ya ce suna da kyakkyawan zato cewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu a shirye ya ke ya yiwa Yan Najeriya aiki shi ya sa ba tare da bata lokaci ba suka amince da bukatunsa ba tare da bata lokaci ba.

Shima Sanata Diket Plang da ga Jihar Plateau ta tsakiya ya nuna goyon bayansa ga  kudurin Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu inv da yace a shirye suke su bashi duk gudunmawar da yake bukata domin a yiwa Yan Najeriya aiki.

20230713 174449

Sai dai Sanata Diket ya ce hakan ba yana nufin za su zama yan amshin Shata bane. Indan bukata ta son zuciya ce ba zasu amince da ita ba.

Daga karshe ya yabawa Yan Najeriya da irin hakuri da suke nunawa da kuma su kara hakuri ce wa kwalliya zata biya kudin sabulu nan bada dadewa ba.

A wani rahoto da kafar BBC ta rawaito ta ce bayan da Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu, na Naira biliyan 500 don rage radadin cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi, yanzu haka ana ci gaba da bayyana ra’ayoyi masu cin karo da juna kan yadda tallafin zai shafi jama’a.

Ita dai gwamnatin shugaban kasar ta tsara cewa za ta rika biyan kimanin mutum miliyan 12 tallafin Naira dubu takwas a duk wata har tsawon watanni shida, domin ganin kudin ya zagaya, arziki ya karu a tsakanin jama’a.

Sai dai wasu daga cikin ‘yan jam’iyyarsa ta APC na ganin ko a gwamnatin baya ta tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari an gwada irin wannan, amma bai yi wani tasiri ba.

Injiniya Sani Bala Tsanyawa, wani dan majalisar wakilai daga jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa sun amince da bukatar ne saboda wannan na daya daga cikin bukatun shugaban na farko, amma ba ya ji hakan zai yi wani tasiri.

A cewarsa: ”Abun a yaba ne farawar da aka yi, amma ko cewa aka yi mutum na daukar albashi ka kara masa Naira dubu takwas, babu wani abu da za ta masa, ballantana kuma mutumin da ko yaushe yana gida babu abun da yake yi.

”Wannan adadi ko kashi goma na ‘yan Najeriya bai kai ba, mutum miliyan goma sha biyu cikin sama da talakawa miliyan dari da hamsin ai ka ga babu abin da aka yi” in ji shi.

Ya nanata cewa akwai bukatar a ce wannan adadi ya fi haka, duba da cewa lamarin ya shafi kowa da kowa ne.

Me jama’a ke cewa?

BBC ta tattauna da wasu mutane da dama a Najeriya don jin ra’ayoyinsu kan wannan al’amari, sai dai yawancinsu na nuna goyon bayansu ne ga duk wani abu da zai zamanto maslaha ga jama’a.

Wani mutum da muka zanta da shi a Abuja, ya ce ”Ba mu da mota ba mu da kudin mai, inda muke biyan Naira dari yanzu Naira dari uku, abun ya shafe mu kwarai da gaske”

”Kare ana biki a gidansu ya ce mu gani a kasa”, in ji ra’ayin wani mutum na daban da shi ma muka zanta da shi

Hatta masu sayar da abinci wadanda harkarsu ta samu nakasu sakamakon yadda farashin komai ya daga na sa ran wannan tallafi zai kai gare ku.

Ita dai gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta fito karara ta yi maganar ga lokacin da za a fara rabon ba, sai dai tuni matasa suka yi kwanto suna jira don cin gajiyar shirin da zarar an fara.

Gwamnatocin da suka gabata na baya ma a Najeriya sun yi wani abu makamancin iran haka, sai dai daga bisani ya kai ga lalacewa ba tare da an ga tasirin hakan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here