Home Uncategorized Ambaliyar Ruwa: An Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Tallafawa Mutanen Nasarawa Ta...

Ambaliyar Ruwa: An Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Tallafawa Mutanen Nasarawa Ta Kudu

111
0
Sen. Onawo 2

An Bukaci Gwamnatin Taraiya da ta kawo dauki na gaggauwa ga kananan hukumomi guda uku da ke Jihar Nasarawawa ta Kudu wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya yi sanadiyyar rasa rai daya da dukiya ta miliyoyin nairori.

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Nasarawa ta Kudu, Sanata Muhammad Ogoshi Onawo ne ya gabatar da wannan bukata a zauren Majalisar Dattawa a jiya Talata a wani kuduri na gaggauwa.

Sanata Onawo da ya ke karawa Yan Jarida haske akan batum cewa ya yi ibtila’in ya shafi kananan Hukumomi guda uku ne da suke yankin nasa kuma anyi asarar rai na mutum guda da dukiya mai yawa.

Ya ce sabo da haka ne ya kawo wannan kuduri gaban Majalisar domin a ja hankalin Gwamnatin Taraiya da ta tallafawa mutanen yankin da abubuwan da ka iya kawo mu su sauki na rayuwa.

Onawa ya  kara da cewa tuni ya rubutawa Hukumar Tallafin Gaggawa ta Kasa NEME da sauran Hukumomi wadanda su ke da alhaki na tallafawa a irin wannan yanayi domin su rage musu radadin rayuwa da su ke fama da shi.

Ya ce halin da mutanen nasa su ke ciki abun a tausaya mu su ne lura da yadda rayuwa ta ke da tsanani a halin yanzu. In da ya kara da cewa da yawa daga cikin wadanda abun ya fadawa dakyar su ke samun abun masarufi domin kullum sai sun fita su ke nemo abun da za su ci, sabo da haka samun kudaden da zasu gyara makwancin da za su kwanta abu ne mai wuya.

A wani bangaren kuma Sanata Ogoshi Onawa, wanda mamba ne na Kwamitin Ma’adanai ya kara mana haske akan gaiyata da kwamitin su ya yiwa Ministan Ma’adanai , inda ya ce sun gaiyaci Ministan ne domin suji irin tsare tsarensa akan bunkasa hanyoyin kudaden shiga ga Kasarnan.

Ya ce a halin yanzu kasarnan ta na bukatar Karin hanyoyin samun kudaden shiga domin gudanar da aiyuka na cigaban kuma Najeriya Allah ya yi mata baiwa da ma’adanai iri-ire. Wanda ya ce kusan dukkanin kananan Hukumomin da suke Kasarnan Allah ya albarkace su da ma’adanai daban-daban.

Dan Majalisar ya kara da cewa, burin Majalisar Dattawa shine tag a ta hada kai da Gwamnatin Taraiya wajen ganin ta samar da dokoki da za su tallafawa yunkurin ta kawo mafita daga halin da Kasarnan take ciki na matsi na tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here