Home Uncategorized Abin da ya sa muka rinƙa ciyo bashi a shekaru 8 na...

Abin da ya sa muka rinƙa ciyo bashi a shekaru 8 na mulkin Buhari

198
0

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ta kare matakin da ta dauka na ciwo basussuka masu dimbin yawa a ciki da wajen kasar a shekaru takwas da ta shafe ta na mulki.

Basussukan da kasar ta ciyo ya sa wasu ‘yan Najeriya da masana tattalin arziki sun nuna damuwa a kan matsalolin da kasar za ta iya fuskanta sakamakon yawan basussukan.

Sai dai ministar kudi da tsare-tsaren tattalin arziki ta kasa ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed ta shaidawa BBC cewa gwamnati ta karɓo bashin ne domin hana kasar faɗawa cikin mawuyacin hali a lokacin da kasar ta samu koma bayan tattalin arziki a shekarun 2016 da 2020.

“Mun samu durkushewar tattalin arzikin kasa sau biyu, a 2016 da 2020 lokacin annobar korona, mun yi iya kokarinmu wajan ganin ƙasar ba ta faɗa cikin mawuyacin hali ba”.

“Saboda kasa mai girma irin Najeriya idan aka barta cikin wannan hali, abin zai baci ne, nesa ba kusa ba”, in ji ta.(BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here