Home Siyasa Abin da ya sa muka dakatar da Iyorchia Ayu – PDP

Abin da ya sa muka dakatar da Iyorchia Ayu – PDP

213
0

Jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da shugabanta na ƙasa, Iyorchia Ayu bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.

Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke ƙaramar hukumar Gboko, a jihar Benue ne suka ɗauki matakin.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kaɗa ƙuri’ar rashin ƙwarin gwiwa kan ayyukansa.

A lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin suka cimma, sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Vanger Dooyum ya ce zagon-ƙasa da Ayu da kuma na kusa da shi suka yi wa PDP ne ya janyo mata shan kaye a gundumar da kuma jihar baki ɗaya, a zaɓen gwamna.

Sun kuma zargi Ayu da rashin biyan kuɗaɗen da ake karɓa na shekara-shekara daga ƴaƴan jam’iyyar, kamar yadda dokokinta suka tanada.

Shugabannin PDP a gundumar, su 12 daga cikin 17 ne suka sanya hannu kan takardar dakatar da shugaban na PDP.

Sun kuma yi zargin cewar Ayu bai kaɗa ƙuri’a ba a lokacin zaɓen gwamna da na ƴan majalisar dokokin jiha da aka gudanar a 18 ga watan Maris, 2023.

Sun ce suna da yaƙinin cewa akasarin na kusa da Ayu sun yi wa jam’iyyar adawa ta APC ne aiki gabanin da kuma lokacin zaɓen, wanda hakan ya sanya PDP ba ta taka rawar a zo a gani ba a gundumar ta Igyorov.

Shugaban PDP a gundumar Igyorov, Kashi Philip da sauran shugabanninta na yankin duk sun sanya hannu kan takardar dakatarwar.

Sai dai shugaban jam’iyyar PDP na jihar Benue, Isaac Mfo ya ce ba ya da masaniya kan dakatarwar.

Ya ce “ban san da wannan batun ba.”

“Babu wani abu makamancin wannan da aka kawo gabana, kuma ba ni da masaniya a kai.”

Shi ma shugaban PDP na ƙaramar hukumar Gboko, Oga Gbangson Adekwagh ya shaida wa manema labaru cewa an tuntuɓe shi kan lamarin sai dai bai san inda labarin ya samo asali ba. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here